"Atiku Ya Hakura da Takara": An Ji Wanda Ya Fi Cancanta PDP Ta ba Tikiti a 2027

"Atiku Ya Hakura da Takara": An Ji Wanda Ya Fi Cancanta PDP Ta ba Tikiti a 2027

  • Ƙungiyar PDP 100 Percent ta bukaci Atiku Abubakar ya bar zancen takara, ya mara wa ɗan takarar Kudu baya domin adalci da daidaito
  • An danganta rugujewar PDP da rawar da Atiku ya taka, musamman jagorancin sauya shekar gwamnoni biyar zuwa APC a shekarar 2014
  • PDP 100 Percent ta ce Kudu na da ƙwararrun matasa da za su iya karawa da Bola Tinubu a zaben 2027, kamar irinsu Gwama Seyi Makinde

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wata ƙungiya mai suna PDP 100 Percent ta roƙi Atiku Abubakar da ya janye daga takarar shugaban ƙasa a 2027, ya goyi bayan dan Kudu.

Ƙungiyar ta bayyana cewa hakan zai taimaka wajen ceto jam’iyyar daga rushewar da take shirin yi, tare da dawo da amincewar al’umma gare ta.

Kungiya ta nemi Atiku ya hakura da tikitin jam'iyyar PDP a zaben 2027
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar. Hoto: @atiku
Asali: Twitter

"Atiku ya hakura da takara" - PDP 100 Percent

Jaridar Vanguard, ta rahoto shugaban ƙungiyar, Dennis Shima, yayin zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Juma'a, yana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Lokaci ya yi da PDP za ta mara wa ɗan takara daga shiyya Kudu baya domin tabbatar da adalci bayan dan Arewa ya yi mulki."

Kungiyar ta nemi Atiku ya hakura da takara saboda zarginsa da zama tushen rikici a jam’iyyar PDP tun lokacin da ya jagoranci gwamnoni biyar suka fice zuwa APC a 2014.

Dennis Shima ya ce:

“Atiku ne ya jagoranci gurguntar da Goodluck Jonathan da PDP lokacin da ya jagoranci gwamnoni suka sauya sheka zuwa APC, ya janyo jam'iyyar ta rasa zaben 2015.”

PDP 100 Percent ta nemi PDP ta kai mulki Kudu

Ƙungiyar ta ce yankin Kudu ba ta mulki kasar na shekaru takwasa ba bayan mulkin dan Arewa, don haka dole a barsu su ma su yi shekaru takwas, idan ana so ayi adalci.

“Yankin Kudu na da matasan 'yan siyasa da suke da cancantar fafatawa da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027, ba dole sai tsofaffi ba.”

- Dennis Shima.

Ya ce dagewa wajen goyon bayan tsofaffin ’yan takara daga Arewa kamar Atiku na iya ƙara ruguza PDP da cire ta daga zukutan jama’a.

Ƙungiyar ta zargi masoyan Atiku da tada jijiyar wuya domin su sake karɓar tikitin shugaban ƙasa, duk da irin barnar da masoyin nasu ya yi.

Kungiyar ta zargi Wike, ta goyi bayan Makinde

Dennis Shima ya ce:

“Da yanzu PDP ta cika shekaru 27 a kan mulki, amma ‘yan 'sabuwar PDP' suka jagoranci faduwar jam’iyyar a 2015.
"Ko a 2023, tarihi ne ya maimaita kansa, domin gwamnonin G5 karkashin Wike sun haddasa rikici a jam’iyyar da rashin haɗin kai wanda ya jawo ta fadi zabe.

Shima ya bukaci PDP ta rungumi matasa irinsu Gwamna Seyi Makinde, ya na mai cewa, “Makinde ya cancanci zama dan takarar shugaban kasa."

A cewar Dennis Shima:

“Rawar da Seyi Makinde ya taka a G5 ya ta'allaka ne kan neman adalci, daidaito da tabbatar da gaskiya a jam’iyyar PDP.”

Ƙungiyar ta PDP 100 Percent ta jaddada bukatar sauya fuska a jam’iyya, ta ce lokaci ya yi da sababbin jini za su karɓi ragamar shugabanci a kasar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.