Tsohon 'Dan Majalisa Ya ba Atiku Muhimmiyar Shawara kan Zaben 2027
- Tsohon ɗan majalisar wakilai, Tajudeen Yusuf ya taɓo batun rigingimun da suka addabi jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya
- Tajudeen Yusuf ya buƙaci Alhaji Atiku Abubakar ya haƙura da yin takara ƙarƙashin PDP a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
- Tsohon ɗan majalisar ya kuma nuna cewa da gangan gwamnonin PDP suka bari rikicin jam'iyyar ya ci gaba da taɓarɓarewa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon ɗan majalisar wakilai, Tajudeen Yusuf, ya ba tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, shawara kan zaɓen 2027.
Tajudeen Yusuf ya buƙaci Atiku Abubakar da ya haƙura da yin takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.

Asali: Facebook
Tsohon ɗan majalisar ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels tv a shirinsu na Sunrise Daily a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wace shawara aka ba Atiku Abubakar?
Tajudeen Yusuf ya buƙaci Atiku da ya haƙura ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP ya fito daga yankin Kudancin Najeriya.
Tsohon ɗan majalisar na ganin cewa lokaci ya yi da Atiku zai janye domin a dawo da tsarin rabon kujeru na asali na PDP wanda a cewarsa zai haifar da zaman lafiya a cikin jam’iyyar.
“Da ina da iko, zan ba tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku shawara, ya ƙyale tikitin PDP, ya bar shi ya koma Kudu. Ko da kuwa ba mu lashe zaɓen shugaban ƙasa ba, za a gan mu a matsayin waɗanda suka koma kan tsarinmu na rabon muƙamai."
“Ka duba Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas waɗanda su ne ginshiƙin jam’iyyar PDP tun da farko, sai kawai ka zo ka ɗauki tikitin takara? Mutane za su fara rasa ƙwarin gwiwa, domin kowa na da burin kaiwa ƙololuwa a aikinsa."
“Idan suka fahimci cewa saboda yawan ƙuri’un da wani yanki ke samu a zaɓen fidda gwanin jam’iyya, ba za su taɓa samun tikitin takara ba, hakan zai sanya su jin takaici."
- Tajudeen Yusuf

Asali: Facebook
Jam'iyyar PDP ta jawowa kanta rikici
Tajudeen Yusuf, wanda ya wakilci mazaɓar Kabba/Bunu/Ijumu a majalisar wakilai, ya bayyana rikicin da PDP ke fuskanta a matsayin wanda su da kansu suka jawowa kansu.
Ya danganta rikicin da ke cikin jam’iyyar PDP da abubuwa da dama, ciki har da gazawar wasu shugabannin jam’iyyar wajen fifita haɗin kan jam’iyyar fiye da muradunsu na siyasa na ƙashin kai.
Hakazalika ya zargi gwamnonin jam’iyyar kan cewa da gangan suka bar lamarin ya tabarbare, domin su samu hujjar barin jam’iyyar zuwa wasu jam'iyyun siyasa.
An buƙaci Atiku ya fice daga PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Olabode George, ya buƙaci Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar.
Olabode George ya yi wannan kiran ne kan abin da ya kira yi wa jam'iyyar PDP zagon ƙasa da tsohon mataimakin shugaban ƙasan yake yi.
Ya soki Atiku kan ziyarar da ya kai wa tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari a gidansa da ke Kaduna.
Asali: Legit.ng