'Yan Hadaka Sun Yi Magana bayan Gwamnan PDP, Abokin Takarar Atiku Sun Koma APC
- Hadakar 'yan hamayya ta ce sauya shekar gwamnan PDP zuwa APC ba sabon abu ba ne, kuma akwai wasu da ke dab da bin sahunsu
- Mai magana da yawun hadakar, Salihu Lukman ya zargi wasu gwamnoni da ke cikin PDP da yin aiki a asirce da Bola Ahmad Tinubu
- Hadakar ta bayyana cewa rikice-rikicen PDP na nuna jam’iyyar ta kauce daga tafarkin da ta saba, amma akwai masu kishi a cikinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jigo a hadakar adawa da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, da Nasir El-Rufai, ke jagoranta, ya yi martani ga gwamnatin tarayya kan sauya shekar gwamnonin PDP.
Ya bayyana cewa sauya shekar Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, da wanda ya gabace shi, Ifeanyi Okowa, da wasu manyan shugabannin jam’iyyar PDP ba sabon abu ba ne ko abin mamaki.

Asali: Facebook
Punch News ta bayyana cewa mai magana da yawun hadakar kuma tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Salihu Lukman, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hadakar Atiku ta caccaki gwamnatin APC
Salihu Lukman ya yi martani ga sukar da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya yi a ranar Litinin.
Mista Onanuga ya yi wa Atiku Abubakar ba’a, yana cewa hadakar da ya ke jagoranta za ta tarwatse bayan sauya shekar abokan tafiyarsa zuwa APC.
Amma Lukman ya kalubalanci wannan magana, yana mai cewa masu magana da yawun fadar shugaban kasa suna mayar da lamarin kamar barkwanci.
"Akwai sauran masu barin PDP," Hadakar Atiku
Tsohon jagora a APC ya kara da cewa, bayan Okowa da Oborevwori, suna da masaniya cewa wasu gwamnoni ma na dab da sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Ya ce:
“Na farko, duk wanda ya ce wannan abu ba a zata ba ne kawai yana yaudarar kansa. Alamu sun riga sun bayyana cewa wasu gwamnoni za su sauya sheka. Ba guda daya ba ne, akwai wasu gwamnoni da dama.
Jam’iyyar PDP ta riga ta rikide, ta tashi daga PDP da aka sani a baya. Ko da yake muna amincewa cewa akwai mutane da shugabanni a PDP da ke da fatan ceto jam’iyyar.”
Hadakar Atiku ta soki gwamnonin PDP
Salihu Lukman ya ci gaba da bayyana cewa suna sane da cewa wasu daga cikin gwamnonin PDP da ke suka hadakar Atiku, suna aiki ne a boye da Asiwaju Bola Tinubu.

Asali: Twitter
Ya ce:
“Amma ku tuna lokacin da gwamnoni suka fitar da wata sanarwa suna sukar hadakar mu, mene ne martaninmu? Mun ce da yawa daga cikinsu suna aiki ne ga Asiwaju.
Bayan haka ne kuka ga sanarwa daga Akwa Ibom, sannan kuma daga Gwamnan Delta. Ba shi kadai ba ne. Idan kuka bi diddigin maganganu, akwai wasu da ake sa ran za su biyo baya.”
Yadda Atiku za zabi Okowa a zaben 2023
A zaben 2023, Atiku Abubakar ya zaɓi Ifeanyi Okowa, gwamnan jihar Delta a lokacin, a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a karkashin jam’iyyar PDP.
Zaɓin Okowa ya biyo bayan dogon tunani da shawara tsakanin manyan jiga-jigan jam’iyyar, inda aka fi karkata zuwa ga dan takarar da zai kawo daidaito a yankunan ƙasa, musamman Kudu.
Duk da cewa wasu 'yan jam’iyyar sun fi son Nyesom Wike na jihar Rivers, Atiku ya zaɓi Okowa saboda dabi'unsa na sassaucin ra’ayi da iya hada kai da kowane bangare.
Hakanan, ana kallon Okowa a matsayin wanda ke da salo na diflomasiyya fiye da Wike, wanda ake zargi da ɗabi’ar takama da tada hankali da suka bambanta da tsarin sulhu da Atiku ke so.
Atiku: 'Yan Hadaka sun caccaki gwamnonin PDP
A wani labarin, mun ruwaito cewa hadakar siyasa da Atiku Abubakar ke jagoranta, ta bayyana rashin jin daɗinta game da yadda gwamnonin PDP ke tafiyar da al’amuran jam’iyyar.
A cewar hadakar, gwamnonin PDP na ƙoƙarin karɓe ikon wasu muhimman sassa na jam’iyyar, lamarin da ta bayyana a matsayin yunƙurin lalata adawa da tabbatar da nasarar Bola Tinubu.
Mai magana da yawun hadakar, Salihu Mohammed Lukman, ya ce hadakar Atiku ce kadai mafita da za ta iya ceto demokuraɗiyyar Najeriya daga halin da take ciki a halin yanzu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng