'Mun Ɗinke 2027': Ganduje Ya Faɗi Lokacin da Wasu Gwamnonin PDP Za Su Dawo APC

'Mun Ɗinke 2027': Ganduje Ya Faɗi Lokacin da Wasu Gwamnonin PDP Za Su Dawo APC

  • Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya ce wasu gwamnoni daga PDP za su sauya sheƙa zuwa jam'iyyar kafin zaɓen 2027 mai zuwa
  • Ganduje ya faɗi haka ne lokacin da yake karɓar Sanata Kawu Sumaila da wasu mambobi daga NNPP da PDP da suka koma jam'iyyar APC
  • Tsohon gwamnan Kano ya ce goyon bayan Bola Tinubu yana ƙaruwa, yana kuma tabbatar da cewa nasarar APC a 2027 "tuni an kammala ta"

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana kan shirin wasu da za su dawo jam'iyyar.

Ganduje ya bayyana cewa wasu gwamnoni daga jam’iyyar PDP za su sauya sheƙa zuwa APC kafin zaben 2027.

Ganduje ya magantu kan shirin zuwan gwamnonin PDP cikin APC
Abdullahi Ganduje ya fadi shirin APC kan zaben 2027 da ke tafe. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Asali: Twitter

Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi Sanata Kawu Sumaila daga Kano ta Kudu, da wasu mutane biyu, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin Sumaila na barin NNPP zuwa APC

Sanata Kawu Sumaila ya ce muradin mutanensa zai fi samun biyan bukata ne a jam’iyyar APC, inda zai ƙara daraja jam’iyyar.

Ya ce:

"Ku koma ku duba sakamakon zaɓen 2023 na shugaban ƙasa, na sanata, da na wakilan majalisa, a rana guda, wuri guda.”
“Na tsaya takara tare da Kwankwaso a wancan wurin. Za ku ga sakamakona, nashi da kuma na sauran wakilai a rana guda.”
“A zaɓen da ya biyo baya na sanata da na majalisar jiha, za ku ga bambancin, kuma za ku fahimci abin da muke faɗa.”

Hangen Ganduje kan sauya sheka zuwa APC

Ganduje ya ce yawaitar sauya sheƙa na nuni da cewa tuni an tabbatar da wa’adi na biyu na Tinubu a shekara ta 2027, Daily Post ta tabbatar.

Ya ce:

“A cikin APC, muna da tabbacin shugabanmu Bola Ahmed Tinubu da sauye-sauyen tattalin arziki da kuma tsarin ‘Renewed Hope’.”

“Yanzu mun buɗe sabon shafi ta hanyar shawarwari da lallashi don samun manyan gwamnoni masu tasiri su shiga APC.”
“Gwamnan Delta ya koma APC tare da majalisar jiha, wakilan tarayya da ma manyan jami’an PDP har da tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.”
Ganduje ya sha alwashi zaben 2027 da nasarar APC
Abdullahi Ganduje ya ce APC ta shirya sosai game da zaɓen 2027. Hoto: All Progressives Congress.
Asali: Facebook

'Gwamnonin PDP za su dawo APC' - Ganduje

Ganduje ya ƙara da cewa APC za ta fadada kuma gwamnonin PDP da dama za su dawo APC mai mulkin Najeriya.

A cewarsa:

“Don haka za ku ga muna faɗaɗa, ba zan bayyana sirrinmu ba, amma nasarar APC a 2027 ta tabbata.”
“Gwamnoni da dama na shirin zuwa APC, kuma a duk inda aka yi zaɓe, APC za ta ci, Insha Allah."

Sumaila: NNPP ta ce ta rabu da raƙai

Kun ji cewa shugaban jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano, Hashim Dungurawa ya yi martani kan sauya sheƙar Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila.

Dungurawa ya bayyana cewa ba su damu ba ko kaɗan da ficewar da sanatan mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa ya yi .

Ɗan siyasar ya bayyana cewa dama tuni sanatan ya zame musu ƙarfen ƙafa kuma sun yi murna da sauya sheƙar da ya yi zuwa APC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.