Kifi na Ganin Ka: Yadda Sojoji Suka Tayar da Hankalin Shugabannin ISWAP
- Manyan kwamandojin ISWAP sun shiga fargaba da zargin juna bayan bayanan sirrinsu sun shiga hannun Rundunar Sojin Najeriya har an wallafa su
- Wani babban kwamandan ISWAP mai suna Ba Shuwa ya bayyana mamakinsa kan yadda sojojin Najeriya suka samu sahihan sunayensu
- Wannan lamari ya kara tayar da zargin cewa jami’an tsaro sun yi masu kutse, sannan ya jefa rashin shakku da zarhin juna a tsakanin manyan ISWAP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno – Rahotanni sun ce manyan kwamandojin ISWAP sun shiga cikin fargaba da zargin juna bayan dakarun Operation OPHK sun fitar da jerin sunaye da hotunan wasu manyan ‘yan ta’addan kungiyar da ake nema ruwa a jallo.
Bayanan sirrin sun nuna cewa matakin ya haifar da matukar damuwa a
Mayakan da ke aiki a yankin tafkin Chadi.

Source: Twitter
Zagazaola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa yanzu haka, wasu kwamandojin kungiyar na tambayar yadda jami’an tsaro suka samu sahihan bayanai kan wasu manyan mambobinsu.
ISWAP ta shiga cikin rudani
A cewar bayanan sirrin, Ba Shuwa, wanda aka bayyana a matsayin daya daga cikin manyan shugabannin ISWAP, ya nuna matukar mamaki kan sahihancin sunaye da hotunan da ke cikin jerin mutanen da ake nema ruwa a jallo.
Ya kuma fara tambayoyi a kan wasu takardun bayanai da dakarun Najeriya suka rarraba a baya-bayan nan wanda ke kunshe da sahihan bayanansu.
Ana ganin martanin nasa ya kara jefa manyan kwamandojin ISWAP cikin fargaba, musamman kan yiwuwar kutsen jami’an leken asiri cikin tsarin shugabanci da ayyukan kungiyar.
Manyan ISWAP sun fara zargin junansu
Majiyoyi sun ce sahihancin bayanan ya haifar da zargi a tsakanin ‘yan ta’addan, inda wasu kwamandoji ke kara nuna damuwa kan yadda aka iya gano sunayensu, inda suke da kuma ayyukan da suke gudanarwa.
Ana sa ran wannan ci gaba zai kara zurfafa rashin amincewa da juna a cikin kungiyar, musamman a daidai lokacin da ake samun rahotannin rashin jituwa da kuma takaddamar shugabanci tsakanin manyan kwamandojin ISWAP a yankin tafkin Chadi.

Source: Facebook
Takardun mutanen da ake nema ruwa a jallo, wadanda rahotanni suka ce sun kunshi hotuna da bayanan tantance wasu kwamandojin ‘yan ta’adda, na cikin wani babban shirin leken asiri da rundunar soji ke amfani.
Majiyoyin tsaro sun ce rarraba wadannan takardu na kuma nufin nuna wa kwamandojin ‘yan ta’addan da abokan huldarsu cewa jami’an tsaro suna da cikakken bayani kan tsarin shugabancin kungiyar.
'Yan ta'addan ISWAP sun sha wuta
A baya, mun kawo labarin cewa rundunar sojin sama ta Najeriya (NAF) ta hallaka mayakan ISWAP tara, ciki har da wani babban kwamanda, a wani samamen sama a jihar Borno d ake Arewa maso Gabas.
An kai samamen ne ranar Asabar, 8 ga watan Agusta, bayan samun bayanan sirri kan motsin ’yan ta’addan a yankin dajin Sambisa wanda ya shahara wajen zama mafakar baya gari da yan kungiyar Boko Haram.
Rundunar sojin saman kasar nan ta ce mutuwar kwamandan na iya kawo cikas ga zirga-zirgar manyan ’yan kungiyar da tsarin tsaron su a yadda siuke kai hare-hare kan al'umma da hana mutane zama lafiya.
Asali: Legit.ng

