Sheriff: Gaskiyar abin da Ya Sa Gwamnan Delta Ya Sauya Sheka daga PDP zuwa APC

Sheriff: Gaskiyar abin da Ya Sa Gwamnan Delta Ya Sauya Sheka daga PDP zuwa APC

  • Sheriff Obovrevwori ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC a jihar Delta, wanda ya kawo ƙarshen mulkin PDP na shekaru 26 a jihar
  • Bayan sanar da sauya shekar, mutane da dama sun cika da son sanin dalilin da ya sa Gwamna Sheriff ya yanke wannan shawara
  • Wani rahoto da Legit Hausa ta gani ya jero wasu dalilai da suka sa Obovrevwori ya koma APC, ciki har da matsalarsa da James Ibori

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Delta - Bayan watanni ana yada jita-jita, gwamnan jihar Delta, Sheriff Obovrevwori, ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC a ranar Laraba.

James Manager, wanda shi ne shugaban farko na PDP a jihar, ya sanar da hakan bayan wani taro da gwamnan ya yi da shugabannin jam'iyyar a Asaba.

Anji ainihin abin da ya sa gwamnan Delta ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC
Gwamnan jihar Delta, Sheriff Obovrevwori da ya sauya sheka daga PDP zuwa APC. Hoto: @RtHonSheriff
Asali: Twitter

Gwamna ya magantu kan dalilin komawa APC

Manager ya bayyana cewa dukkanin dukkanin shugabannin PDP na jihar sun amince da wannan sauyi a wajen taron, inji rahoton Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa wannan sauyin yana da alaƙa da rikicin shugabanci na ƙasa a PDP da yadda hakan zai shafi jam'iyyar a zaben 2027.

A cewarsa, PDP na cikin wani hali a yanzu, domin tana da gwamnoni kimanin 11 ne kawai, kuma ba za su iya doke shugaban ƙasa a 2027 ba.

Obovrevwori a nasa bangaren, ya bayyana cewa, bayan nazarin siyasar jihar da ya yi, ya yanke shawarar canza sheƙa saboda matsalolin da ke addabar PDP.

Duk korafin Obovrevwori da abokan hulɗarsa kan rikicin shugabanci na PDP, an ce akwai wasu dalilan da suka sa ya yanke shawarar komawa APC.

Sabanin Obovrevwori da tsohon gwamnan Delta

Rahoton ya nuna cewa daya daga cikin dalilan sauya shekar shi ne Obovrevwori ya sa samun goyon bayan tsohon gwamnan jihar, James Ibori, wanda shi ne kusar PDP a jihar.

James Ibori ya ki goyon bayan Obovrevwori a zaben fidda gwani na 2022, wanda hakan ya jefa gwamnan cikin wani yanayi na tsaka mai wuya.

Duk da cewa Obovrevwori ya lashe zaben 2023 ba tare da goyon bayan Ibori ba, amma an ce kusancin Ibori da Shugaba Bola Tinubu ya kara jefa Obovrevwori a matsala.

An ce Tinubu, yana da wasu manyan masu iko a jihar, ciki har da Tompolo, wanda ke goyon bayan APC, wanda hakan ya tilasta Obovrevwori ya canza sheƙa a karshe.

Alakar binciken EFCC da sauya shekar Obovrevwori

Obovrevwori ya ga cewa zama cikin APC yana da muhimmanci domin samun goyon bayan gwamnatin tarayya da kuma kariya daga masu adawa a PDP.

Hakan ya biyo bayan rikicin siyasa da ya barke a PDP, wanda ya kai ga sauya sheƙar wasu shugabanni, ciki har da Sanata Ned Nwoko.

An kuma ce binciken da EFCC ke yi kan tsohon gwamnan jihar, Ifeanyi Okowa, na daga dalilan da ya sa shugabannin PDP suka yanke shawarar hada kai da APC.

Ba a bayyana ko EFCC za ta rufe binciken da take yi a kan tsohon gwamnan ba, amma dai wasu suna ganin cewa APC na bude kofar tuba ga membobinta.

An ji dalilan da suka sanya gwamnan Delta ya fice daga PDP zuwa APC
Gwamnan jihar Delta, Sheriff Obovrevwori. Hoto: @RtHonSheriff
Asali: Facebook

Ainihin abin da ya jawowa gwamna barin PDP

Majiya ta bayyana cewa, babban dalilin da ya sa Obovrevwori ya sauya sheƙa shi ne fahimtar cewa PDP ta durkushe a jihar Delta bayan mulkinta na tsawon shekaru.

PDP ta sha kaye a zaben shugaban kasa na 2023 a jihar Delta, duk da cewa gwamnan jihar, Okowa, yana tare da PDP a matsayin abokin takarar Atiku Abubakar.

PDP ta kuma sha kaye a wasu kujeru na majalisar dattijai ga APC, duk da cewa ta samu nasara a zaben gwamna da kuma wasu kujeru na majalisar wakilai.

Hakan yana nuni da yadda PDP ta sauka daga matsayinta na jam'iyyar da ke da rinjaye a jihar Delta.

Obovrevwori ya ga cewa kasancewa cikin APC zai ba shi damar samun goyon bayan gwamnatin tarayya da kuma kawar da adawar da zai iya fuskanta daga PDP.

'Tinubu ya kulla yarjejeniya da gwamnonin PDP'

A wani labarin, mun ruwaito cewa, majiyoyi na zargin ce an kula wata yarjejeniya ta sirri tsakanin Shugaba Tinubu da wasu gwamnonin jam'iyyar PDP.

An ce gwamnonin PDP, musamman wadanda yanzu suke a wa'adin farko, sun yarda su marawa Tinubu baya a sirrance, da zummar zai taimaka musu su zarce a 2027.

Majiyoyin na zargin gwamnonin Bauchi, Adamawa, Oyo da Filato za su iya kware wa PDP baya a zaben 2027 idan jam'iyyar ta ba Atiku Abubakar tikitin takara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.