Fadar Shugaban Kasa Ta Ragargaji Atiku, El Rufa'i kan Hadakar Kifar da Tinubu
- Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa burin Atiku Abubakar na siyasa ya fara dusashewa bayan wasu 'yan PDP sun koma APC
- Ya ce manyan abokan tafiyarsa sun fara juya masa baya, ciki har da tsohon gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa da suka yi takara tare a zaben 2023
- Fadar shugaban kasa ta ce PDP na cikin rikici, kuma hadakar ta mutu tun kafin ta yi karfi saboda rashin amincewar da take fuskanta daga ‘yan siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Bayan ficewar wasu jiga-jigan PDP zuwa APC da kuma cigaba da rikicin cikin gida, wani hadimi na musamman ga shugaba Bola Tinubu ya ce tafiyar Atiku Abubakar ta ruguje.
Fadar shugaban kasa ta yi magana ne yayin da wasu 'yan siyasa na kokarin hadaka a lokacin da wasu ke tururuwar komawa APC.

Asali: Getty Images
Daya daga cikin masu magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya bayyana cewa hadakar Atiku ba za ta yi nasara ba a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce duk wani yunkuri da Atiku ke yi tare da wasu ‘yan siyasa kamar Nasir El-Rufai da Babachir Lawal ya ci tura, saboda yawancin wadanda ya ke fata za su mara masa sun juya masa baya.
Onanuga ya ce tafiyar Atiku ta rushe
Onanuga ya ce Atiku, El-Rufai, Babachir Lawal da Hakeem Baba-Ahmed na ƙoƙarin hada gungun siyasa, amma gungun nasu ya riga ya wargaje tun kafin ya hadu.
A sakon da ya wallafa, Onanuga ya ce:
“Tafiyar siyasar Atiku ta samu matsala. Hadakar da ya ke kokarin kafa wa da El-Rufai da Babachir da Baba-Ahmed ta riga ta tarwatse.
"Tsofaffin abokan tafiyarsa kamar Ifeanyi Okowa da mambobin CPC sun guje shi. Atiku zai sake faduwa,”
Ya yi wannan tsokaci ne a matsayin martani ga wani sako da wani hadimin shugaban kasa, Tunde Rahman ya wallafa a X.
Tunde Rahaman ya bayyana cewa sauya sheƙa da wasu shugabannin PDP suka yi ya jefa Atiku cikin wani mawuyacin hali.

Asali: Facebook
Siyasar Atiku da masu sauya sheka
Tunde Rahman ya bayyana ficewar tsohon gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, da gwamna mai ci Sheriff Oborevwori zuwa APC a matsayin koma baya ga Atiku.
The Cable ta wallafa cewa Tunde Rahaman ya ce:
“Tabbas, yanzu gwamnonin PDP suka fara komawa APC... Shin hadakar Atiku ba ta mutu tun kafin ta fara aiki ba?
"Lallai haka ne, kamar yadda mutanenmu ke cewa, duk wata Juma’ar da za ta yi kyau, daga Laraba ake gane ta.”
Legit ta tattauna da Adamu Ahmed
Wani matashi mai kokarin ganin an yi hadaka a 2027, Adamu Ahmed ya bayyana wa Legit cewa maganar da fadar shugaban kasa ta fada ba lallai ta tabbata ba.
A cewar Adamu:
"Kamar yadda ake komawa APC a yanzu, a nan gaba kadan za a ga wasu na shiga jam'iyyun adawa, dama haka siyasa ta gada.
"Sauya sheka ba alama ba ce ta nasara, akwai shekara biyu a gaba, wanda komai zai iya sauyawa a cikinsu."
Hakeem Baba-Ahmed ya rubuta wasika ga Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mashawarci a fadar shugaban kasa, Hakeem Baba Ahmed ya bukaci Tinubu ya hakura da takarar 2027.
Dr. Hakeem ya bayyana cewa lokaci ya yi da Bola Tinubu zai kafa tarihin ba matasa damar yin takara a 2027 domin kawo cigaba.
Ya kuma soki salon mulkin Bola Tinubu, musamman wajen raba mukamai da mu'amala da mutane wajen isar musu da sakon gwamnati
Asali: Legit.ng