G100: An Fara Shirin Hada Kan Atiku, Obi da 'Yan Adawa Don Tsayar da Dan Takara 1 a 2027
- G-100 za ta gudanar da taron hadin kan jam’iyyun adawa a Abuja ranar 18 ga watan Agusta, 2026, gabanin zaben 2027
- Kungiyar ta gana da shugabannin jam’iyyun adawa shida domin tattauna yadda za a samar da hadin kai
- G-100 ta ce hadin kan adawa zai bukaci sadaukarwa da sassauci daga shugabannin jam’iyyun na adawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wata kungiyar jam’iyyun siyasa da masu ruwa da tsaki na adawa karkashin dandalin G-100 za ta gudanar da taron koli a Abuja ranar 18 ga watan Agusta, 2026, domin kokarin samar da hadin kan jam’iyyun adawa gabanin babban zaben 2027.
Taron na zuwa ne bayan jerin shawarwari tsakanin wakilan G-100 da shugabannin jam’iyyun adawa shida, wadanda suka hada da ADC, APM, NDC, PRP da SDP.

Kara karanta wannan
'Yan sanda sun cafke fasto da sojoji kan shirya sace matan manyan malaman addini a Plateau

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Salihu Lukman ya sanya wa hannu a madadin G-100 ranar Litinin, 10 ga watan Agustan 2026, cewar rahoton The Punch.
Kungiyar ta ce shawarwarin sun samar da ginshikin zurfafa tattaunawa kan yadda jam’iyyun adawa za su hada kai wajen gabatar wa ’yan Najeriya wani sahihin zabin da zai maye gwamnatin yanzu a zaben 2027.
Sanarwar mai taken G100: Consultations with opposition leaders set stage for unity summit ta ce wakilan kungiyar sun gana da shugabannin jam’iyyun na kasa, ’yan takarar shugaban kasa da abokan takararsu.
G-100 ta gana da shugabannin adawa
Kungiyar ta ce an gudanar da shawarwarin ne da gangan ba tare da kafofin yada labarai ba, domin bai wa ’yan siyasar damar tattauna batutuwa masu muhimmanci cikin ’yanci ba tare da matsin lambar jama’a ba.
G-100 ta ce an samu matsaya daya daga cikin tarurrukan, musamman kan bukatar jam’iyyun adawa su shawo kan sabanin da ke tsakaninsu tare da kafa wani tsari na siyasa mai hadin kai gabanin zaben 2027.
“Daga cikin wadannan tattaunawa, an fahimci karara cewa akwai bukatar jam’iyyun adawa na Najeriya su kara aiki tare gabanin babban zaben 2027,” in ji kungiyar.
Hadin kai zai bukaci sadaukarwa
Sai dai G-100 ta amince cewa samar da hadin kan adawa zai bukaci jam’iyyun da shugabanninsu su yi wasu manyan rangwame, The Cable ta kawo rahoton.
Kungiyar ta ce shugabannin da aka tuntuba sun fahimci cewa sahihiyar adawa mai tasiri za ta samu ne kawai ta hanyar “sadaukarwa, sassauci da kuma shirye-shiryen fifita muradun kasa fiye da kananan bukatun jam’iyya ko na mutum”.

Source: Twitter
Ana sa ran taron kolin da aka shirya gudanarwa ranar 18 ga watan Agusta zai samar da damar fara tattaunawa kan hanyoyin da jam’iyyun za su kara yin hadin gwiwar siyasa.
Rikici ya kunno kai tsakanin Atiku da ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa rikici na neman barkewa tsakanin Atiku Abubakar da jam'iyyarsa ta ADC kan zaben 2027.
Rahotanni sun ce jam’iyyar adawa ta ADC da dan takarar na ta na shugaban kasa, sun samu sabani kan wanda ya kamata ya jagoranci yakin neman zabensa.
Asali: Legit.ng
