PDP Ta Rikice: Magoya bayan Wike Sun Ware Gefe, Sun Nada Shugabannni a Jihohi 2
- Rikicin PDP a Kudu maso Kudu ya tsananta yayin da bangaren Nyesom Wike ya kafa sababbin shugabanni a jihohin Bayelsa da Edo
- Rikicin ya samo asali ne daga zaben fidda gwani na Edo, inda Dan Orbih da magoya bayansa suka nuna adawa da takarar Asue Ighodalo
- Yayin da PDP karkashin Umar Damagum ta dakatar da Orbih, shi kuma ya ware gefe, ya kafa shugabannin jam'iyyar a jihohin biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo - Rikicin da ke addabar jam’iyyar PDP a Kudu maso Kudu ya dauki sabon salo yayin da bangaren da ke biyayya ga Nyesom Wike, ya kafa sababbin shugabanni a Edo da Bayelsa.
Jam’iyyar PDP a yankin ta kasu gida biyu: daya na karkashin Chief Dan Orbih wanda Wike ke marawa baya, daya kuma karkashin Chief Emmanuel Ogidi wanda kwamitin NWC ya amince da shi.

Asali: Facebook
Rikicin zaben fitar da gwanin PDP a Edo
Jaridar Daily Trust ta ce wannan rikici ya samo asali ne tun bara, bayan takaddamar da ta biyo bayan zaben fidda gwani na gwamna a jihar Edo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Chief Dan Orbih da mabiyansa sun bayyana adawa da dan takarar jam’iyyar, Dr Asue Ighodalo, saboda sabanin da ke tsakaninsa da tsohon gwamna Godwin Obaseki.
Sakamakon hakan, kwamitin NWC ya dakatar da Orbih daga jam’iyyar, kamar yadda muka ruwaito.
Kakakin jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba, ya ce an dauki matakin ne bayan taron NWC karo na 588.
Daga nan ne aka kafa kwamitin mutane shida karkashin jagorancin mataimakin shugaban jam’iyya na Kudu, Ambasada Taofeek Arapaja, domin bincikar Orbih.
Rikicin taron jam'iyyar PDP a Calabar
Duk da dakatarwar, Orbih da magoya bayansa sun gudanar da taron zartarwa na Kudu maso Kudu a Calabar a watan Fabrairu, wanda Wike ya halarta.
A wannan taron, an sake zaben Orbih a matsayin shugaban yankin, lamarin da PDP, karkashin jagorancin Damagum ta ce ba ta amince da shi ba.
Ologunagba ya bayyana taron na Calabar a matsayin “taronta jama’a” kawai, yana mai jaddada cewa PDP ba ta amince da wani taron yanki ba.
Ya kawo hujjoji daga sashe na 29 (2)(b) da 31 (2)(c) da (j) na kundin tsarin mulkin jam’iyyar, yana mai cewa tuni aka dage taron da aka shirya yi na ranar 22 ga Fabrairu.
Bayan wannan ne, shugaban riko na jam’iyyar na kasa, Umar Damagum, ya kaddamar da kwamitin riko da zai kula da harkokin PDP a yankin Kudu maso Kudu.
Umar Damagum ya ce taron da aka gudanar a ranar 22 ga Fabrairu, wanda Orbih ya sake samun mukamin shugaban yankin “bai inganta ba.”
Rikici kan gangamin jam'iyyar PDP a Bayelsa
Rikicin jam'iyyar ya kara kamari a Bayelsa yayin da magoya bayan Wike suka yi yunkurin shirya gangami domin girmama shi, amma gwamnatin jihar ta dakatar da hakan saboda dalilan tsaro.
An ce an shirya taron ne kuma domin gode wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa nade-naden mukamai ga ’yan asalin jihar.
Sai dai, babbar kotun jihar ita ma ta bayar da umarnin hana gudanar da taron, duba da cewa a ranar ne magoya bayan Gwamna Diri suka shirya gangami.
An rahoto cewa, donmin kauce wa rikici da kuma mutunta umarnin kotun, magoya bayan Wike suka dage nasu gangamin.

Asali: Twitter
Bangaren Wike ya kafa sababbin shugabanni
A tsakiyar wannan rudani ne, a ranar Talata, kwamitin aiki na yanki (ZWC) da ke biyayya ga Wike karkashin jagorancin Orbih, ya sanar da kafa sababbin shugabanni a Bayelsa da Edo.
A cewar sakataren yada labarai na yanki, Etim Isong, an dauki matakin ne bayan rushe kwamitin gudanarwa na jihar Bayelsa da na riko a Edo saboda “gazawar shugabannin na shawo kan rikice-rikicen jam’iyya.”
A Bayelsa, George Turnah ne shugaban sabon kwamitin rikon, Tony Gabriel a matsayin mataimaki, sai Ebilade Ekerefe a matsayin sakatare.
A Edo kuwa, Nosa Ogieva ne shugaban kwamitin, Chief Sunny Okomayin na matsayin mataimaki, sai Hillary Otsu a matsayin sakatare.
An fara kira a kori Wike daga PDP
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar kwararrun mambobi a PDP ta bukaci a gaggauta korar Ministan Abuja, Nyesom Wike daga jam’iyyar.
Sun ce Wike na ci gaba da yin karan tsaye da nuna goyon baya ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu duk da kasancewarsa dan PDP.
Kungiyar ta kuma yi barazanar daukar matakin shari’a kan Wike bisa zargin cin mutuncin jam’iyyar da kuma muzanta wasu mambobinta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng