Yarjejeniyar da Ake Zargin Tinubu da Wasu Gwamnonin PDP Sun Kulla gabanin 2027

Yarjejeniyar da Ake Zargin Tinubu da Wasu Gwamnonin PDP Sun Kulla gabanin 2027

  • Rikicin a PDP na ci gaba da ɗaukar zafi, bayan zargin wata yarjejeniya ta sirri tsakanin Shugaba Tinubu da wasu gwamnonin jam'iyyar
  • An ce gwamnonin PDP, musamman masu wa'adin farko, sun amince da taimakawa Tinubu, shi kuma zai taimaka musu su zarce a 2027
  • Majiyoyi na zargin gwamnonin Bauchi, Adamawa, Oyo da Filato za su juya wa PDP baya idan ta ba Atiku Abubakar tikitin takara a gaba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Majiyoyi sun bayyana cewa rikicin shugabanci da ya ki ci ya ki cinye wa a babbar jam’iyyar adawa ta PDP ba zai lafa nan kusa ba.

Majiyoyin na ganin rikicin zai ci gaba da mamaye PDP ba saboda wata "yarjejeniyar sirri" tsakanin Shugaba Bola Tinubu da wasu gwamnonin jam'iyyar.

Majiyoyi na zargin cewa Tinubu da wasu gwamnonin PDP sun kulla yarjejeniya gabanin 2027
Shugaba Bola Tinubu (Hagu), wasu gwamnonin jam'iyyar PDP (Dama). Hoto: @AdamawaLas79384, @officialABAT
Asali: Twitter

'Yarjejeniya tsakanin Tinubu da gwamnonin PDP'

Jaridar The Sun ta rahoto cewa wasu gwamnonin PDP, musamman wadanda ke wa’adi na farko, sun amince da taimakawa Tinubu tare da sun fice daga jam’iyyar ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, ko a makon da ya gabata, jiga-jigan jam'iyya mai mulki ta APC sun karyata wannan ikirari tare da cewa babu wata yarjejeniya tsakanin Tinubu da gwamnonin PDP.

Sai dai, majiyoyi daga jam'iyyar ta adawa sun dage kan cewa akwai wata yarjejeniyar 'sirri' da aka gwamnonin PDP, musamman masu wa'adin farko suka kulla da Tinubu.

Kalaman gwamnan Akwa Ibom kan Tinubu

Wata majiya ta shaida cewa:

“Shugaban ƙasa zai samu goyon bayan gwamnonin PDP ba tare da sun sauya sheƙa ba. Za su taimaka masa a jihohinsu, shi kuma zai taimaka musu wajen sake lashe zaɓe.
"Idan za ku tuna, gwamnan Akwa Ibom ya tabbatar da hakan kwanan nan, inda ya ce: 'Ni ba na baki biyu. Ranar can na ce maku ina tare da Bola Tinubu.

"Wasu su na ce mun kar na ce haka, amma kuma su ne ke zagaye wa suna zuwa wurin Baba suna fada masa cewa za su goya masa baya, abin mamaki, da rana kuma su nuna akasin haka.”
"Ni a matsayata, zan goyi bayan Baba ya yi tazarce a 2027. Idan lokaci ya yi zan bayyana maku dalili, amma yanzu lokaci bai yi ba."

Gwamnonin da ake zargin su na tare da Tinubu

Majiyoyi sun ce Tinubu zai ba gwamnoni goyon bayansa a 2027, yayin da su kuma za su tabbatar da nasararsa a jihohin, abin da majiyar ta kira da “Ban gishiri in ba ka manda."

Majiyar ta ce matakin tsohon gwamnan Rivers, Nyesom Wike na zama inuwa daya da Tinubu ya sa shugaban kasar ya samu gindin zama a cikin PDP.

An ce gwamnonin jihohin Adamawa, Filato, Bauchi da Oyo na tare da Wike wajen goyon bayan Tinubu, musamman idan Atiku ya sake samun tikitin jam’iyyar PDP.

Rikicin gwamnan Bauchi da Atiku Abubakar

Majiyar ta ce:

“Wike da Bala Mohammed ba sa ga-maciji yanzu, amma idan Atiku ya sake samun tikiti, tabbas za su yi aiki tare don goyon bayan Tinubu.”

Idan ba a manta ba, gwamnan Bauchi, Bala Mohammed ya ce ba zai yi aiki da wanda bai goya masu baya a zabukan baya ba, yana nuni da Atiku da ya goyi bayan ɗan takarar APC a jihar.

Ɗan Bala Mohammed ya fito ya kara da cewa:

“Ba za mu goyi bayan Atiku ba, ya yi wa mahaifina zagon ƙasa a zaɓen gwamna ta hanyar goyon bayan dan takarar APC.”
Ana zargin wasu gwanonin PDP za su goyawa Tinubu baya a 2027 ba tare da sun fita daga jam'iyyar ba
Gwamnonin PDP a wani taro da suka gudanar a jihar Oyo. Hot: @AdamawaLas79384
Asali: Twitter

Tinubu na kara samun karfi a majalisar tarayya

Majiyoyi sun ce Wike na da hannu a rikicin da ya dabaibaye batun nadin sabon sakataren PDP na ƙasa, lamarin da ke ci gaba da ƙara jawo rabuwar kawuna a jam'iyyar.

Majiyar ta ce:

“Ko hana muzuru ana shaho, PDP ba za ta iya hana Tinubu zarcewa ba. Wannan ne ya sa aka kulla yarjejeniyar tsakanin ɓangarorin biyu.”

Rahoto ya nuna cewa tun 1999, babu wata jam’iyya da ta lashe zaɓen shugaban ƙasa ba tare da ficewar ‘yan siyasa da haɗin gwiwa tsakanin jam’iyyu daban-daban ba.

Yanzu haka, Tinubu na ƙara samun rinjaye a majalisar tarayya sakamakon sauya sheƙar da ake samu, wanda ke kara alamta cikar burinsa na yin tazarce a 2027.

Gwamnan Delta ya fice daga jam'iyyar PDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnan jihar Delta, Hon. Sheriff Oborevwori, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki.

Sanarwar ta biyo bayan wata ganawa ta sirri da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Asaba, inda manyan jiga-jigan APC suka tarbe shi cikin farin ciki.

Gwamna Oborevwori ya ce sauya shekar za ta ƙarfafa haɗin gwiwar siyasa da kawo ci gaban jihar Delta a manyan matakai na gwamnati.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.