"Dimokuraɗiyya na cikin Haɗari": Bugaje Ya Fallasa Dabarar APC na Jawo Ƴan Adawa

"Dimokuraɗiyya na cikin Haɗari": Bugaje Ya Fallasa Dabarar APC na Jawo Ƴan Adawa

  • Jam'iyyar APC mai mulki na amfani da kuɗi wajen yaudarar manyan ‘yan PDP su sauya sheka, inji tsohon dan majalisa, Usman Bugaje
  • Bugaje ya ce amfani da kudi ko kuma barazana wajen tilastawa 'yan adawa sauya sheka zuwa APC yana barazana ga dimokuraɗiyya
  • Tsohon hadimin shugaban kasar ya soki yadda PDP ta yi martani ga sauya shekar gwamnan Delta, inda ya ce jam'iyyar ta rasa karfinta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kuma ɗan majalisa a baya, Usman Bugaje, ya fallasa dabarar da APC ke amfani da ita wajen jan ra'ayin 'yan adawa.

A cewar Usman Bugaje, APC na amfani da kuɗi wajen yaudarar manyan ’yan jam'iyyar PDP su sauya sheka.

Dr. Usman Bugaje, ya zargi APC da amfani da kudi da barazana wajen janyo 'yan adawa
Usman Bugaje, tsohon dan majalisa daga jihar Katsina. Hoto: @Ahmadlori
Asali: Twitter

Bugaje ya zargi APC da sayen 'yan adawa

Tsohon dan majalisar ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi kai tsaye a tashar Arise TV ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Usman Bugaje ya nuna damuwa kan yadda siyasa ke komawa kasuwanci, yana mai cewa hakan na barazana ga dimokuraɗiyyar Najeriya.

"A yadda na sani, duk da ba na da’awar cewa na san komai, APC na amfani da kuɗi wajen sayen 'yan PDP," inji Bugaje.

Bugaji ya ƙara da cewa wasu lokuta, ana amfani da barazana wajen tilastawa 'yan adawa sauya sheka, musamman ga waɗanda ke fuskantar bincike daga EFCC.

"Dimokuradiyya na cikin hadari" - Bugaje

Ya kara da cewa:

"Idan mutum yana da matsala a EFCC, sai a fara masa barazana. Wannan salon siyasa tun zamanin Obasanjo ake yin sa.

Bugaje ya bayyana damuwa cewa amfani da kuɗi wajen janyo mutane na nuni da rugujewar dimokuraɗiyya a ƙasar Najeriya.

"Idan kuɗi ne ke yanke hukunci a siyasa, to wannan ba dimokuraɗiyya ba ce. Za mu iya fadawa hanyar Peru da Fujimori," inji Bugaje.

Bugaje ya yi magana kan tabarbarewae PDP a matsayin jam'iyyar adawa
Dr. Usman Bugaje. Hoto: @Ahmadlori
Asali: UGC

Bugaje ya alakanta tabarbarewar PDP da Wike

Bayan sauya shekar gwamnan Delta, shugaban PDP, Umar Damagum, ya ce jam’iyyar ba ta yi zaton hakan ba, amma ya ce zaɓe mai zuwa zai zama tsakanin 'yan Najeriya da APC.

To sai dai, Bugaje ya soki martanin PDP, yana mai cewa kadarin jam’iyyar ya karye tun bayan rikicin da ministan Abuja, Nyesom Wike ya jawo.

"Tun daga lokacin da ministan Abuja, Wike ya aikata abin da ya yi, PDP ta rasa damar zama babbar jam’iyyar adawa," inji Bugaje.

Ya kuma zargi PDP da gazawa wajen taka rawar gani a muhimman batutuwan kasa kamar majalisar tarayya da tattaunawar kasafin kuɗi.

Kalli hirar a nan kasa:

'Mulkin Tinubu ya fusata 'yan Najeriya' - Bugaje

A wani labarin, mun ruwaito cewa, a ci gaba da bayyana ra’ayoyi kan shekara ɗaya da Bola Ahmed Tinubu ya yi a mulki, Usman Bugaje ya yi tsokaci mai zafi.

Ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta nuna gazawa cikin shekara ɗaya, inda ta kasa cika manyan abubuwan da ta ɗauki alkawari a kai.

Dr. Bugaje ya kuma bayyana wasu hanyoyi da za a bi don dakile tabarbarewar al’amura da kare Najeriya daga fadawa cikin matsanancin hali.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.