2027: Alkawura 2 da Jam'iyyar APC Ta Yi Wa Gwamnan Delta bayan Ya Shigo Cikinta

2027: Alkawura 2 da Jam'iyyar APC Ta Yi Wa Gwamnan Delta bayan Ya Shigo Cikinta

  • Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi maraba da sauya sheƙar gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori zuwa cikinta
  • APC ta ce sauya sheƙar da gwamnan ya yi, ta sanya yanzu jihar Delta za ta ba da cikakkiyar gudunmawa wajen cimma manufofin gwamnatin Bola Tinubu
  • APC ta yi alƙawarin ga Gwamna Sheriff Oborevwori tare da sauran masu sauya sheƙar cikakken haɗin kan da ya dace

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta yi magana kan sauya sheƙar da gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya yi zuwa cikinta.

Jam'iyyar APC ta nuna farin cikinta kan sauya sheƙar zuwa cikinta, inda ta ce za a ba Gwamna Oborevwori cikakken gurbi da damar da ta dace.

Oborevwori ya koma APC
Jam'iyyar APC ta yi maraba da sauya shekar Gwamna Sheriff Oborevwori Hoto: @RtHonSheriff
Asali: Twitter

Mai magana da yawun jam’iyyar APC na ƙasa, Felix Morka, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Laraba, a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Felix Morka ya ce yanzu jihar Delta ta shirya tsaf domin bayar da cikakkiyar gudunmawa ga nasarar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Me APC ta ce kan sauya shekar gwamnan Delta?

A cikin sanarwar APC ta yi alƙawarin ba gwamnan da sauran masu sauya sheƙar cikakkan haɗin kai da gurbin da ya dace a cikinta.

"Kwamitin gudanarwa na ƙasa na jam’iyyar APC, ƙarƙashin jagorancin mai girma, Abdullahi Umar Ganduje, CON, na matuƙar farin ciki da matakin da gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya ɗauka na shiga wannan babbar jam’iyya tamu."
"Ya shigo tare da fitattun shugabannin jam’iyyar PDP, ciki har da tsohon gwamnan jihar Delta kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na PDP a zaɓen 2023, Sanata Ifeanyi Okowa, manyan jami’an gwamnati."
"Tare da shugabanni da ƴan majalisar dokoki, shugabannin ƙananan hukumomi da kansiloli a jihar, da kuma ɗumbin shugabanni da mambobin PDP.
"Babbar jam’iyyarmu tana maraba da wannan muhimmin ci gaba da hannu biyu-biyu, kuma tana tabbatarwa gwamnan da shugabannin PDP samun cikakken haɗin kai da gurbi a jam’iyyar APC ta jihar Delta."

Sheriff Oborevwori
Sheriff Oborevwori ya koma APC Hoto: @RtHonSheriff
Asali: Facebook
"Da wannan mataki, wanda ya zo a daidai lokacin da shugabanni da mambobin PDP a faɗin jihar ke ci gaba da sauya sheƙa zuwa APC, ciki har da mambobin ƙungiyar Delta Unity Group daga mazaɓar tarayya ta Ika."
"Muna cikin farin ciki cewa jihar Delta yanzu da ta koma jihar APC ta shirya bayar da cikakkiyar gudunmawa ga nasarar cikar manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da kuma ci gaba mai ɗorewa da bunƙasar al’ummar Delta da dukkan ƴan Najeriya."

- Felix Morka

Abokin takarar Atiku ya koma APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa abokin takarar Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Ifeanyi Okowa, ya fice daga jam'iyyar PDP.

Sanata Ifeanyi Okowa ya sauya sheƙa ne zuwa jam'iyyar APC tare da gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori.

Sauya sheƙar ta su ta kawo ƙarshen shekarun da jam'iyyar PDP ta kwashe tana mulkar jihar Delta mai arziƙin mai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng