Sheriff da Wasu Gwamnonin Najeriya da Suka Sauya Jam'iyya Lokacin Suna kan Mulki
- Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta ya fice daga PDP zuwa APC a hukumance, lamarin da ake ganin zai yi tasiri sosai a 2027
- A tsawon lokaci, gwamnoni da dama sun sauya sheƙa yayin da suke kan mulki, ciki har da Aminu Tambuwal, Abdulfatah Ahmed da sauransu
- Gwamnoni a jihohi kamar Zamfara, Adamawa, Sokoto, da sauransu sun sha sauya jam'iyya, wanda ke nuna rashin tabbacin siyasa a Najeriya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Delta - A ranar Laraba, gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP mai adawa zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Wannan ba shi ne karon farko da aka samu gwamna mai ci ya sauya sheka daga jam'iyyar da ya lashe zabe zuwa wata jam'iyyar ba.

Asali: Facebook
A tsawon shekaru, gwamnonin jihohi da dama sun sauya jam’iyya yayin da suke kan mulki, kamar yadda rahoton Punch ya nuna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnonin da suka sauya sheka suna kan mulki
Mun tattaro wasu daga cikin gwamnonin Najeriya da suka sauya jam'iyya a lokacin da suke kan mulki:
1. Sheriff Oborevwori
Kamar yadda muka ruwaito, Gwamna Sheriff Oborevwori ya ci zaɓen gwamna 2023 ne a ƙarƙashin jam’iyyar PDP.
Sai dai kuma a wata sanarwa da ta ba kowa mamaki a ranar Laraba, gwamnan, kwamishinoninsa, da mukarrabansa suka fice daga PDP, suka koma APC a hukumance.
Sanata James Manager da kwamishinan yaɗa labaran jihar, Aniagwu Charles, sun tabbatar da sauya sheƙar, lamarin da suka ce zai yi tasiri sosai ga 2027.
2. Aminu Waziri Tambuwal
A shekarar 2018, aka ruwaito cewa Aminu Waziri Tambuwal, lokacin yana gwamnan Sokoto, ya sauya sheka daga APC zuwa PDP.
An ce Tambuwal, bayan saukarsa daga mulki, ya nemi tikitin takarar kujerar shugaban ƙasa karkashin PDP, amma Atiku Abubakar ya doke shi.
Sai dai, ba Tambuwal ne kadai gwamnan Sokoto da ya sauya sheƙa ba. Sauran da suka sauya sheƙa daga jihar Sokoto sun haɗa da:
3. Attahiru Bafarawa: ANPP zuwa PDP
4. Aliyu Wamakko: PDP zuwa APC
5. Abdulfatah Ahmed (Kwara)
A shekarar 2013 aka rahoto cewa gwamnan Kwara (na wancan lokaci), Abdulfatah Ahmed ya fice daga PDP zuwa APC sannan kuma ya koma PDP a 2018.
A wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar 31 ga Yulin 2018, Abdulfatah ya ce:
"Bayan tattauna da masu ruwa da tsaki a jihar, na koma PDP domin APC ba za ta iya ci gaba da zama jam'iyyar da zan cika muradun jama'a ta ba."
6. Boni Haruna (Adamawa)
Boni Haruna ya yi gwamnan jihar Adamawa ne daga shekarar 1999 zuwa 2007, kamar yadda rahoton The Nation ya nuna.
A lokacin da ya ke kan mulki, an rahoto cewa Gwamna Boni Haruna ya sanar da fiewarsa daga jam'iyyar PDP zuwa AC.
7. Ikedi Ohakim (Imo)
Ikedi Ohakim ya zama gwamnan jihar Imo a zaben 2007. An ce ya sauya sheka daga jam’iyyar PPA zuwa PDP a lokacin da yake kan mulki.
8. Murtala Nyako (Adamawa)
An rahoto cewa Murtala Harauna Nyako ya rike gwamnan Adamawa daga shekarar 2007 zuwa 2008. Abin mamaki, shi ma ya fice daga APC zuwa PDP.
9. Rochas Okorocha (Imo)
An zaɓi Rochas Okorocha a matsayin gwamnan jihar Imo a 2011. Ya fice daga jam’iyyar APGA zuwa APC a lokacin mulkinsa.
10. Mahmuda Shinkafi (Zamfara)
A lokacin da Mahmuda Shinkafi ya ke gwamnan jihar Zamfara, ya sauya sheka daga ANPP zuwa PDP, a karshe bai samu tazarce ba.

Asali: Facebook
11.Bello Matawalle (Zamfara)
Bello Matawalle, a lokacin da ya ke matsayin gwamnan jihar Zamfara, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP zuwa APC.
Har yanzu yana cikin jam'iyya APC, kuma yana daya daga cikin ministocin gwamnatin Bola Tinubu.
Haka kuma, jihohin Benue, Ondo, Rivers, Cross River, Edo, Kano, Kebbi, da Jigawa duk sun fuskanci sauya sheƙar gwamnoni masu ci a lokuta daban-daban.
Alkawuran da APC ta yi wa gwamnan Delta
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam’iyyar APC mai mulki ta yi maraba da Gwamna Sheriff Oborevwori, wanda ya shiga jam'iyyar bayan ficewarsa daga PDP.
Jam’iyyar ta ce wannan sauyin shekar zai baiwa jihar damar bayar da gudunmawa mai muhimmanci wajen cimma burin gwamnatin Bola Tinubu.
APC ta kuma tabbatar da cewa za ta baiwa Oborevwori da sauran masu sauya sheƙa cikakken haɗin kai da goyon baya a sabuwar tafiyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng