‘Yan Jam’iyya Sun Yi Watsi da Batun Sulhu, Babu Ranar Ganin Karshen Rikicin NDC
- Fusatattun mambobin NDC daga jihar Edo sun fito fili sun ki aminta da kwamitin sulhun da jam'iyyar ta kafa masu
- Mambobin sun bayyana cewa kafa kwamitin yunkuri ne kawai na tilasta musu karbar sakamakon zaben fitar da gwani
- ‘Yan jam’iyyar jaddada cewa ba za a samu zaman lafiya ko hadin kai na gaskiya a kwamitin Pat Utomi da Buba Galadima
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - Wasu fusatattun ‘ya ‘yan jam’iyyar NDC a yankin Kudancin jihar Edo sun yi fatali da zancen sulhu da aka kawo.
Jam’iyyar hamayyar ta kafa kwamitin sulhu na kasa domin sasanta sabanin da aka samu, sai dai hakan bai kawo mafita ba.

Source: Twitter
Ana zargin NDC da rashin adalci a Edo
Vanguard ta rahoto cewa wadanda ake rikici da su sun yi watsi da kwamitin da aka kafa, suna cewa an yi masu rashin adalci.

Kara karanta wannan
Nasara daga Allah: Sojoji da yan sanda sun rutsa yan bindiga fiye da 200 ta sama da ƙasa
A cewarsu, kafa wani kwamiti ba zai kawo karshen rikicin ba tunda aka dauke takararsu bayan nasararsu a zaben tsaida gwani.
Mista Agbonaye Osazee Ofo ya fitar da jawabi a madadin gungun ‘ya ‘yan jam’iyyar da ake rigima da su a kudancin jihar Edo.
"Yunkurin jam’iyyar NDC na kafa kwamitin sulhu na kasa biyo bayan zaben tsaida gwaninta, wani yunkuri ne da yake kokarin nuna wa a fili cewa ana son kawo zaman lafiya da hadin-kai a jam’iyyar.
"Sai dai bayan abin da aka nuna wa duniya, akwai babban abin tambaya a kasa. Su wa za a sasanta kuma a kan wani gwadaben?
"Kwamitin sulhu ba zai maye gurbin adalci ba. Ba za a iya amfani da shi a madadin zaben tsaida gwani, a rufe bakin koken jama’a ba, ko a tursasa wa ‘yan jam’iyya su rungumi abin da aka kakaba masu."
- Agbonaye Osazee Ofo

Source: Twitter
Kwamitin Buba Galadima zai sasanta NDC?
Jawabin ya ce ba a kafa kwamitin saboda a samu sulhu ba, sai dai kawai da nufin a tursasa amincewa da matakin da NDC ta yanke.
Agbonaye Osazee Ofo ya ce ba za ta yiwu a murde zaben tsaida gwani, sannan a tilasta wa kowa amincewa da karfa-karfar ba.
Ofo ya yi gargadi cewa idan babu adalci, ba za a taba samun wani hadin-kai a jam’iyyar NDC ba.
An ce a cikin ‘yan kwamitin sulhun akwai Farfesa Pat Utomi da Injiniya Buba Galadima, wadanda sun yi fice sosai a fagen siyasa.
Duk da haka, masu korafin sun ce wadannan mutane ba za su iya magance rashin adalcin da aka yi ba ta hanyar zaman kwamitinsu.
‘Yan jam’iyyar suna ganin kwamitin bai cin gashin kan sa kuma bai da hurumin sake duba abin da ya faru wajen zaben tsaida gwani.
Idan ba za a sake duba sakamakon zaben fitar da ‘yan takara ba, Ofo da mutanensa suna ganin ba za a taba samun zaman lafiya ba.
ADC ta shiga rikicin takara a Adamawa
Rikicin cikin gida ya sake tsananta a jam'iyyar ADC reshen jihar Adamawa kan batun 'sauya' sunan dan takarar gwamna a shafin INEC.
Rahoto ya zo cewa jam’iyyar ADC ta burma rudani da canjin ‘dan takara, ta ba Modibbo Tukur Ribadu a tikin gwamnan Adamawa a zaben 2027.
Kwamitin yakin zaben Suleman Umar ya karyata rade-radin da ake ji, ya ce har yanzu suna takara a ADC.
Asali: Legit.ng

