Hukumar yan sandan NAjeriya
Rundunar yan sanda reashen jihar Legas ta tabbatar da mutuwar mataimakin kwamishina, Khan Salihu, an ce ya koma gida bayan fitowa daga masallaci ranar Lahadi.
Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar ta lalata wasu bama-bamai da ake zargin 'yan bindiga suka dasa a kan titin Kunchin Kalgo da ke karamar hukumar Tsafe.
'Yan bindiga dauke da makamai sun yi aika-aika a jihar Neja. Hatsabiban sun kona gidajen mutane tare da hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Wasu 'yan bindiga sun kutsa kauyen Ode Oriya da ke Owo a jihar Ondo, inda suka sace Baalen garin, Adeniyi Adelana, da dare tare da bindige matarsa yayin harin.
A labarin nan, za a ji cewa Boko Haram ta kai mummunan hari ƙaramar hukumar Chibok da ke jihar Borno inda aka kone wadansu makarantu a harin da ba a saba gani ba.
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana shirin daukar sababbin jami’an tsaro 50,000 tare da ware N5.41tn domin inganta tsaro a Najeriya. Ya fadin hakan a ranar dimokuradiyya.
Gwamnan Oyo, Seyi Makinde ya bayyana cewa bayanan sirri sun nuna cewa har yansu daliban da yan bindiga suka sace na nan a cikin gandun daji na Old Oyo National Park.
Jami'an tsaro a jihar Kogi sun tabbatar da mutuwar fitaccen ɗan bindiga da akae kira Ibrahim Baccujo bayan an dakile yunkurin sace ɗaliban WAEC a Iluke.
Majalisar wakilai ta amince da kudirin kafa rundunar ‘yan sandan jihohi a Najeriya bayan ‘yan majalisa 288 sun kada kuri'ar goyon bayan wannan kudiri.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari