Mutane Sun Huta, Jami’an Tsaro Sun Yi Ajalin Hatsabibin Dan Bindiga, Baccujo

Mutane Sun Huta, Jami’an Tsaro Sun Yi Ajalin Hatsabibin Dan Bindiga, Baccujo

  • Rundunar yan sanda a Kogi sun tabbatar da mutuwar fitaccen ɗan bindiga bayan an dakile yunkurin sace ɗaliban WAEC a Iluke
  • Jami'an ‘yan sanda suka ce an kashe wani hatsabibi ma yayin samamen hadin gwiwar jami'an tsaro kan miyagun yan ta'adda
  • Hukumomin tsaro sun yaba da hadin kai tsakanin jami'ai, tare da gode wa Gwamna Ahmed Usman Ododo kan goyon bayan tsaron Kogi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lokoja, Kogi - Rundunar ‘yan sanda a Kogi ta tabbatar da mutuwar fitaccen jagoran ‘yan bindiga wanda ya addabi al'ummar yankuna da dama a jihar.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa hatsabibin dan bindiga, Ibrahim Baccujo na daga cikin yan ta'adda da suka kai hari a Iluke wanda a dauki hankulan al'umma.

An kashe babban dan bindiga a Kogi
Marigayi hatsabibin dan bindiga, Ibrahim Baccujo da sufeta-janar na yan sanda, Rilwan Disu. Hoto: @zagazOlamakama, Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Sanarwar da jami'ar hulda da jama'a ta rundunar, ASP Saliu Oyiza Afusat, ta fitar ta ce wannan nasara ta samo asali ne daga hadin kai, cewar NTA News.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunan hari wurin da dalibai ke yin jarabawar WAEC a Kogi

Yadda marigayin ya yi yunkurin sace dalibai

An ce maharan sun yi yunkurin sace ɗaliban da ke rubuta jarabawar WAEC tare da wasu mazauna yankin, amma jami'an tsaro suka dakile harin.

Ta bayyana cewa bayanan sirri sun tabbatar Ibrahim Baccujo ya mutu sakamakon raunukan da ya samu a musayar wuta da jami'an tsaro a yankin.

Sanarwar ta kuma tabbatar da cewa wani fitaccen ɗan bindiga mai suna Isa Mai Dabbaba ya rasa ransa yayin wannan samame na hadin gwiwa.

A cewarta, wannan ci gaba ya nuna irin tasirin hadin kai da kyakkyawar mu'amala tsakanin hukumomin tsaro da mutane a Kogi inda ta bukaci jama'a su ci gaba da ba da goyon baya.

Hatsabibin dan bindiga a mutu a Kogi
Taswirar jihar Kogi da yan bindiga ke yawan kai hare-hare. Hoto: Legit.
Source: Original

Yan sanda sun yabawa jami'anta kan farmakin

Rundunar ta yaba da jarumtaka, ƙwarewa da jajircewar jami'an tsaro da suka halarci wannan aiki domin kare rayuka da dukiyoyi, kamar yadda Zagazola Makama ya wallafa a X.

Ta kuma gode wa Gwamnan Kogi, Ahmed Usman Ododo, bisa ci gaba da ba da goyon baya wajen ƙarfafa tsarin tsaro a jihar.

Kara karanta wannan

Sace dalibai: Gwamna ya umarci rufe makarantu bayan samun rahoton DSS

Rundunar ta sake jaddada cewa ta hanyar ci gaba da hadin kai da ƙuduri, Kogi za ta ci gaba da zama wuri mai wahala ga masu aikata laifuffua kowane iri a jihar.

Ta tabbatar da cewa jihar za ta kasance cikin aminci da kwanciyar hankali ga dukkan ‘yan ƙasa masu bin doka da oda yayin da rundunar ke kokarin kare rayuka da dukiyoyi.

Ya bindiga sun kashe babban soja a Kaduna

A baya, an ji cewa wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne da suka tuba daga ayyukan ta'addanci a baya sun kashe sojoji takwas ciki har da wani.

Laftanan a Kaduna An ce sojojin sun fada komar 'yan bindigar ne yayin da suke kan hanyar zuwa kai daukin gaggawa a wasu yankunan Chikun da Igabi.

Harin ya sake tayar da kura kan tsarin Gwamnatin Najeriya na sulhu da 'yan bindiga da kuma na sake mayar da ‘yan bindiga cikin al’umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.