Zaben 2027: Yan Sanda Sun Tura Sako ga Masu Daukar Nauyin Bangar Siyasa

Zaben 2027: Yan Sanda Sun Tura Sako ga Masu Daukar Nauyin Bangar Siyasa

  • Rundunar ’yan sandan Katsina ta gargadi masu daukar nauyin bangar siyasa cewa za ta gano su, ta gudanar da bincike tare da kama su
  • Ta ce za ta gudanar da aikinta ba tare da nuna tsoro ko la'akari da jam'iyya ba domin tabbatar da an samu zaman lafiya mai dorewa a jihar
  • Rundunar ta bukaci matasa da su guji bari a yi amfani da su wajen tada rikici, kai hare-hare kan abokan hamayya ko kawo cikas ga tsarin zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina - Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta gargadi ’yan siyasa da sauran mutanen da ke daukar nauyin tashin hankalin siyasa gabanin babban zaben 2027.

Ta yi barazanar cewa za ta gano su, ta gudanar da bincike tare da kama su, ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasar da suke goyon baya ba.

Kara karanta wannan

Yadda sojoji suka ceto bayin Allah a Kebbi da wasu jihohi 2 daga yan bindiga

Yan sandan jihar Katsina sun gargadi matasa
Wasu daga cikin yan sandan Najeriya Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Jaridar Punch ta kawo labarin cewa rundunar ta gargadi matasa da kada su bari ’yan siyasa su yi amfani da su wajen tada hankalin jama’a.

Sakon yan sandan Katsina ga matasa

A rwayar Daily Post, rundunar ta bukaci matasa su ki amincewa da duk wani tallafi ko tukuicin da aka ba su domin tarwatsa gangamin siyasa, tsoratar da abokan hamayya ko kawo cikas ga tsarin zabe.

Kwamishinan ’yan sandan Katsina, CP Ali Fage, ne ya yi wannan gargadin a cikin jawabin da mataimakinsa, DCP Aminu Gusau, ya gabatar a madadinsa yayin bikin Ranar Matasa ta Duniya ta 2026.

An gudanar da taron ne a ranar Alhamis,20 ga watan Agusta, 2026 inda matasa da wakilan hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya da kungiyoyin fararen hula suka halarta.

Yan sanda sun zaburar da matasa

Kwamishinan ya ce yayin da zaben 2027 ke kara karatowa, akwai bukatar matasa su kasance cikin shirin ko-ta-kwana, musamman ganin yadda suke cikin wadanda aka fi kokarin daukar aiki wajen aikata tashin hankali da sauran laifuka.

Kara karanta wannan

APC, ADC da jam'iyyun da suka bayyana shirinsu na fara yakin neman zaben shugaban kasa

An nemi matasa su guji shiga bangar siyasa
Taswirar jihar Katsina a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya ce rundunar ta kaddamar da wani shiri mai taken “Makomata ta fi siyasa muhimmanci”, domin dakile tashin hankalin siyasa, daba, magudin zamani da kuma amfani da matasa wajen cimma manufofin siyasa.

Kwamishinan ya ce:

“Yayin da muke tunkarar shekarar babban zabe, akwai barazana mai bangarori uku da ke yin barazana ga burinmu na zaman lafiya, wato tashin hankalin siyasa na zahiri da kuma tashin hankalin siyasa na zamani."

'Yan sanda sun kai hari Katsina

A baya, kun ji cewa sama da mazauna Unguwar Guru 3,000 sun tsere daga gidajensu bayan sabbin hare-haren ‘yan bindiga a karamar hukumar Kankia ta jihar Katsina.

Mazauna sun ce an kashe mutane 13 tare da yin garkuwa da mata da ‘yan mata a hare-haren da aka kai ranar Asabar da Litinin wato 15 zuwa 17 ga watan Agusta, 2026.

‘Yan gudun hijirar sun kwashe sama da kwanaki tara a Rimaye ba tare da samun wani tallafi daga gwamnatin jihar ko tarayya ba Read more:

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng