An Yi Musayar Wuta da 'Yan Daba Suka Farmaki Ayarin Motocin Gwamna Adeleke
- Wasu da ake zargin ’yan daba ne sun kai hari kan tawagar Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun bayan ya kammala ziyarar fadar Ataoja na Osogbo
- An yi musayar harbe-harbe tsakanin jami’an tsaron gwamnan da maharan na tsawon kusan mintuna 12 zuwa 15
- Gwamnatin jihar Osun ta tabbatar da harin, tana mai cewa jami’an tsaron gwamnan sun yi artabu mai zafi da maharan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Osogbo, Osun - Wasu da ake zargin ’yan daba ne sun kai hari kan tawagar Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke
'Yan daban sun kai harin ne jim kadan bayan Gwamna Adeleke ya bar fadar Ataoja na Osogbo, Oba Jimoh Oyetunji, inda aka yi musayar harbe-harbe da jami’an tsaron gwamnan.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa lamarin ya faru ne jim kadan bayan Adeleke ya bar dakin taro na fadar, inda ya gana da basaraken.
Adeleke ya je fadar Ataoja
Adeleke ya isa fadar Ataoja da misalin karfe 3:15 na yamma cikin ayarin motoci kusan 20 bayan ya bar hedikwatar hukumar zabe ta kasa (INEC) da ke Osogbo, inda aka ba shi takardar shaidar lashe zabe bayan sake zabarsa.
Wata ganau da ta nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce Oyetunji ne ya tarbi Adeleke da tawagarsa a fadar.
A cewar ganau din, gwamnan ya gabatar wa basaraken takardar shaidar lashe zaben da ya samu.
Yadda harin ya faru
Ganau din ta ce lamarin ya fara ne yayin da ganawar ke dab da kammala bayan basaraken ya yi addu’a.
Ta ce Adeleke ya riga ya fita daga dakin taron ta wata kofa da aka ware domin basaraken da matansa kafin aka fara jin karar harbe-harbe.
“Ya riga ya shiga motar bas da ta kawo shi da wasu na kusa da shi fadar lokacin da muka fara jin karar harbe-harbe mai karfi. Wadanda suka kai harin sun zo ne cikin wata motar Sienna ba tare da lambar rajista ba ta yankin Ita Olokan da ke Osogbo."
“An kwashe kusan mintuna 12 zuwa 15 ana harbe-harben kafin ayarin gwamnan ya bar fadar. Jami’an tsaron gwamnan da ’yan daba sun yi musayar harbe-harbe. Daga bisani ’yan daban suka tsere daga wurin.” In ji ta.
Wata ’yar kasuwa da ke kusa da fadar, wadda aka bayyana sunanta da Munirat kawai, ta ce maharan na iya samun labarin ziyarar Adeleke ne sannan suka jira isowarsa.
“Muna zargin wadannan ’yan daban sun ji labarin ziyarar Adeleke kuma suka jira isowarsa. Sun zo ne cikin wata motar Sienna. Har ma sun lalata babbar kofar fadar. Sun yi harbi kan babbar kofar fadar, amma jami’an tsaro suka fatattake su.” In ji ta.
Gwamnati ta tabbatar da harin
Da aka tuntubi Kwamishinan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Jihar Osun, Kolapo Alimi, ya tabbatar da harin.
Alimi ya ce jami’an tsaron gwamnan sun yi nasarar fatattakar maharan, inda ya tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa a lamarin.

Source: Original
An yi wa Adeleke addu'ar nasara
A wani labarin kuma, kun ji cewa mahaifin mawaki Davido, Deji Adeleke ya ce ya yi addu’a domin ganin ɗan’uwansa, Gwamna Ademola Adeleke, ya sake lashe zaɓen gwamnan jihar Osun.
Deji ya ce maimakon ƙoƙarin yin gogayya da APC wajen kashe kuɗi, ya koma ga Allah ya roƙe shi ya ba ɗan’uwansa nasara.
Asali: Legit.ng

