Gwamnatin Najeriya Ta Yi Magana kan Sayar da Litar Fetur a N200

Gwamnatin Najeriya Ta Yi Magana kan Sayar da Litar Fetur a N200

  • Gwamnatin tarayya ta ce matatar Dangote ba za ta iya fara aiki yadda ya kamata ba idan har ana ci gaba da sayar da fetur kan kasa da N200
  • Ministan kudi, Taiwo Oyedele, ya ce cire tallafin fetur ya haifar da wahala, amma ya taimaka wajen samar da yanayin da masu zuba jari za su yi aiki
  • Oyedele ya ce da ba a cire tallafin ba, Najeriya za ta iya fuskantar karancin fetur, yayin da farashinsa zai iya kaiwa N3,000 a kasuwar bayan fage

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa matatar Dangote ba za ta iya fara gudanar da harkokinta yadda ya kamata ba idan har Najeriya ta ci gaba da tsarin tallafin fetur da farashin litar mai bai wuce N200 ba.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Trump ya kaddamar da sabon salon yaki da Iran

Ministan kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arzikin Najeriya, Taiwo Oyedele, ya bayyana hakan ne yayin wani taro da aka gudanar a Abuja ranar Laraba.

Taiwo Oyedele da Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da ministan kudi, Taiwo Oyedele. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Punch ta rahoto cewa Oyedele ya ce cire tallafin fetur da kuma sauya tsarin kasuwar canjin kudin waje sun jefa 'yan Najeriya cikin wasu matsaloli, amma ya ce sauye-sauyen sun taimaka wajen kauce wa wata babbar matsalar tattalin arziki.

Managar sayar da fetur a N200

Oyedele ya ce da gwamnati ta ci gaba da sayar da fetur kan kasa da N200 a kowace lita, zai yi wahala matatar Dangote ta iya sayar da man da ta tace cikin tsarin da zai ba ta damar samun riba.

Ya ce a tsarin da aka saba da shi, gwamnati za ta sayar da fetur da aka shigo da shi daga kasashen waje a farashi mai tallafi, yayin da kamfanin da ya samar da fetur zai jira gwamnati ta biya sauran kudin.

Oyedele ya ce:

"Ku tuna cewa muna shigo da man fetur daga waje. Wannan yana nufin matatar Dangote ba za ta iya fara aiki ba, domin ba za ku iya sayar da lita kan N200 ba sannan ku zauna kuna jiran gwamnati ta biya sauran sama da N1,000."

Kara karanta wannan

Tiriliyoyin Naira ta Tinubu ya adana wa yan Najeriya dalilin cire tallafin mai

Mutane na sayen mai a Najeriya
Yadda mutane ke sayen man fetur a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya ce tsarin zai sanya matatar Dangote cikin wahalar gogayya da fetur din da ake shigo da shi ana sayarwa a farashin da gwamnati ta tallafa.

Maganar kan tallafin fetur

Ministan ya ce ci gaba da sayar da fetur mai tallafi a kan kusan N200 ba yana nufin 'yan Najeriya za su ci gaba da samun mai cikin sauki ba.

A cewarsa, da Najeriya ta ci gaba da tsarin da ake bi kafin sauye-sauyen tattalin arziki, akwai yiwuwar fetur ya zama babu shi a gidajen mai duk da cewa farashinsa na hukuma zai kasance kusan N185.

BBC ta rahoto cewa Oyedele ya ce a irin wannan yanayi, mutane za su iya tilasta sayen litar fetur kan kusan N3,000 a kasuwar bayan fage saboda karancinsa.

Nateriya ta tara N15.8tn

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ce cire tallafin fetur ya taimaka wajen samar da N15.8tn ga tarayyar Najeriya tsakanin watan Yunin 2023 zuwa Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Farashin buhun siminti a Najeriya ya fi sauran kasashen Afrika har gwamnati ta shiga bincike

Taiwo Oyedele ya ce kudin da aka samu sakamakon cire tallafin sun kara yawan albarkatun da ke shiga hannun gwamnatin tarayya da sauran bangarorin tarayya.

Hakan na zuwa ne yayin da 'yan Najeriya ke cigaba da tambayoyi game da inda gwamnatin kasar ta sanya makudan kudin da ta ce an tara bayan cire tallafin mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng