'Yar Mu Ce,' Pantami Ya Taya Maryam Dan'azumi Murnar Cin Gasar Kur'ani a Saudi

'Yar Mu Ce,' Pantami Ya Taya Maryam Dan'azumi Murnar Cin Gasar Kur'ani a Saudi

  • Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya taya Malama Maryam Ibrahim Dan'azumi murnar lashe gasar Al-Qur'ani ta duniya da aka gudanar a Makkah
  • Maryam ta yi fice ne a bangaren mata na haddar izu 60 da tafsiri, inda ta lashe kyautar Riyal 300,000, kwatankwacin kusan Naira miliyan 120
  • Pantami ya kuma bayyana farin cikinsa ganin cewa 'yar'uwar Maryam, Hajara Ibrahim Dan'azumi, ita ma ta taba lashe wata gasar Al-Qur'ani ta duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe – Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya taya Malama Maryam Ibrahim Dan'azumi, 'yar jihar Gombe, murnar babban nasarar da ta samu a gasar Al-Qur'ani ta duniya karo na 46 da aka gudanar a birnin Makkah na kasar Saudi Arabiya.

Maryam ta wakilci Najeriya a gasar, inda ta zama ta farko a bangaren mata na haddar izu 60 da kuma tafsirin Al-Qur'ani.

Kara karanta wannan

'Yar jihar Gombe ta yi zarra a duniya, Maryam ta lashe gasar Kur'ani a Saudi

Maryam Dan'azumi da Sheikh Isa Ali Pantami
Sheikh Isa Ali Pantami a hagu da Maryam Dan'azumi a dama. Hoto: Abba Sani Pantami|Yusuf Muhammad Dukku
Source: Facebook

A cikin sanarwar da Farfesa Suleiman Mohammed ya fitar a madadin Pantami a Facebook, an bayyana nasarar Maryam a matsayin abin farin ciki da alfahari ga iyalanta, jihar Gombe da Najeriya baki daya.

Maryam da Hajara sun kafa tarihi

Nasarar Maryam ta zo ne bayan 'yar'uwarta, Malama Hajara Ibrahim Dan'azumi, ta taba kawo wa Najeriya wata irin nasara a shekarar 2024.

Hajara ta zama wadda ta lashe gasar Al-Qur'ani ta kasa da kasa ta Hashemite karo na 18 da aka shirya domin mata a kasar Jordan.

Bayan wannan nasara, Farfesa Pantami ya bai wa Hajara mota a matsayin kyauta tare da ba ta tallafin karatu har zuwa lokacin da za ta kammala jami'a.

Sanarwar ta ce tun a shekarar 2024 Pantami ya biya tallafin karatun Hajara gaba daya, domin tabbatar da cewa ta samu damar ci gaba da karatunta ba tare da wata matsala ba.

Abin da Pantami ya ce kan ilimi

Kara karanta wannan

Abubuwan da ya dace a sani game da yarjejeniyar da aka yi tsakanin Musulmi da Kiristocin Najeriya

A bayanin da ya yi, Farfesa Pantami ya bayyana cewa ya dade yana bai wa ilimi da kuma tallafa wa matasa muhimmanci.

Ya yi imanin cewa idan aka bai wa matasa goyon baya da kwarin gwiwar da suka dace, za su iya samun manyan nasarori tare da kawo wa iyalansu, al'ummominsu da kasarsu martaba.

A cewar sanarwar, ganin 'yan'uwa mata biyu daga gida daya sun yi fice a gasar Al-Qur'ani ta kasa da kasa wani babban abin farin ciki ne.

An bayyana cewa nasarar Maryam ta nuna irin baiwa da damar da matasan jihar Gombe da Najeriya baki daya ke da su idan aka ba su damar bunkasa.

Maryam Dan'azumi da Yusuf Dukku
Maryam Dan'azumi da ta lashe gasa da Yusuf Dukku a Saudiyya. Hoto: Yusuf Muhammad Dukku
Source: Facebook

Maryam ta samu kyautar miliyoyi

Gasar da aka gudanar karo na 46 ta gudana ne karkashin jagorancin Sarkin Saudi Arabiya, Salman bin Abdulaziz Al Saud.

Ma'aikatar Harkokin Addinin Musulunci ta Saudi Arabiya ce ta shirya gasar, wadda ta samu mahalarta maza da mata 334 daga kasashe 133.

A baya dai Legit Hausa ta wallafa cewa wannan shi ne mafi yawan mahalarta da gasar ta taba samu tun bayan kafuwarta.

Kara karanta wannan

Zaben Osun: INEC ta sanar da dan takarar da ya lashe zaben gwamna

An kuma gode wa gwamnatin Saudi Arabiya karkashin jagorancin Sarki Salman da Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, saboda bai wa Maryam kyautar Riyal 300,000, wanda aka kiyasta ya kai kusan Naira miliyan 120.

Inuwa zai karrama Maryam

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana farin cikinsa kan nasarar da Maryam Ibrahim Dan'azumi ta samu a gasar Al-Qur'ani ta duniya.

Maryam, daliba ce a makarantar Abubakar Siddiq da ke unguwar Herwagana a Gombe, inda ta wakilci Najeriya a gasar da aka gudanar a Makkah.

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce Maryam ta fara lashe gasar a matakin karamar hukumar Gombe, sannan ta zama ta farko a jihar Gombe da Najeriya kafin daga bisani ta wakilci kasar a gasar kasa da kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng