Tinubu Zai Kashe Naira Tiriliyan 5 kan Tsaro, Za a Dauki Sababbin Ƴan Sanda 50000

Tinubu Zai Kashe Naira Tiriliyan 5 kan Tsaro, Za a Dauki Sababbin Ƴan Sanda 50000

  • Shugaba Bola Tinubu ya sanar da shirin daukar sababbin ‘yan sanda sama da 50,000 domin karfafa tsaro a Najeriya baki daya
  • Gwamnatin tarayya ta ware N5.41tn a kasafin 2026 domin bangaren tsaro, mafi girma da aka taba ware wa fanni a tarihin Najeriya
  • Tinubu ya gargadi ‘yan bindiga da masu garkuwa cewa su mika wuya ko su fuskanci karfin gwamnatin Najeriya cikin gaggawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da shirin daukar sababbin jami’an ‘yan sanda sama da 50,000 da kuma dubban sojoji domin karfafa tsaro a fadin Najeriya.

Tinubu ya bayyana hakan ne a jawabin ranar Dimokuradiyya, inda ya nuna damuwa kan sace dalibai da aka yi a jihohin Oyo da Borno.

Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnati za ta dauki sababbin 'yan sanda 50,000
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na rattaba hannu kan wata takarda a Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Za a dauki sababbin 'yan sanda 50,000

Kara karanta wannan

Gwamna Makinde ya bayyana wurin da aka boye dalibai da malaman da 'yan bindiga suka sace

Ya ce duk da al’ummar kasar na cikin damuwa kan hakan, gwamnati na da yakinin cewa za a kubutar da yaran cikin koshin lafiya, in ji rahoton Vanguard.

“Ko da yake an gudanar da bikin bana cikin yanayin damuwa saboda sace yaranmu a Oyo da Borno, muna da yakini cewa za su dawo lafiya,” in ji shugaban kasar.

Shugaban kasar ya jaddada cewa tsaro na daga cikin ginshikan dimokuradiyya, yana mai cewa ba za a samu ci gaba mai dorewa ba idan jama’a na rayuwa cikin tsoro.

“Dimokuradiyya ba ta da karfi idan babu tsaro,” in ji Tinubu.

Tinubu ya ce gwamnatinsa ta ayyana dokar ta-baci a bangaren tsaro tare da daukar matakan karfafa tsarin tsaron kasar baki daya.

Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta amince da daukar sababbin jami’an ‘yan sanda sama da 50,000 tare da dubban sojoji domin bunkasa ayyukan tsaro.

An ware N5.41tn domin tsaro a kasafin 2026

Tinubu ya kuma bayyana cewa an ware Naira tiriliyan 5.41 a kasafin kudin shekarar 2026 domin bangaren tsaro da tsare kasa.

A cewarsa, wannan shi ne mafi girman kudin da aka taba warewa bangaren tsaro a tarihin Najeriya, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

June 12: Tinubu ya ce a caccake shi, amma ya fadi abin da ba ya so a yi

“Gwamnatinmu a shirye take ta kara daukar matakai domin kare rayuka da dukiyoyin ‘yan Najeriya,” in ji Tinubu.
Shugaba Bola Tinubu ya gargadi 'yan ta'adda da su mika wuya ko su fuskanci fushin gwamnati.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana jawabi. Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Tinubu ya gargadi ‘yan ta'adda

Shugaban kasar ya kuma aika da sako mai zafi ga ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da kuma masu daukar nauyin ta’addanci.

Tinubu ya bukaci 'yan bindiga da masu garkuwa da su mika wuya ko kuma su fuskanci fushin gwamnati.

Shugaban ya ce:

“Ga ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da masu daukar nauyin ta’addanci: Ku mika wuya ko ku fuskanci cikakken karfin gwamnatin Najeriya.
“Ba za a ci gaba da bude kofar afuwa har abada ba. Ba za a nuna jin kai ga masu zubar da jinin ‘yan Najeriya ba.”

Tinubu zai gyara wutar Najeriya

A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya ce an bai wa kwamitin musamman na fadar shugaban kasa kan harkokin wutar lantarki izinin ware makudan kudi a bangaren.

Tinubu ya umarci kwamitin ya ware Naira tiriliyan huɗu ta hanyar domin biyan ingantattun tsofaffin basussukan bangaren wutar lantarki a Najeriya.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin jawabinsa na Ranar Dimokuraɗiyya, inda ya ce an ɗora wa kwamitin alhakin magance matsalolin ƙarancin kuɗaɗe a harkar harkokin wutar lantarki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com