'Yan Sanda Sun Lalata Shirin Kai Harin Bama Bamai kan Matafiya a Jihar Zamfara
- Rundunar ’yan sandan Zamfara ta gano wasu bama-baman da ake zargin ’yan bindiga ne suka dasa a kan titin jihar
- Rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaro sun lalata abubuwan fashewar cikin nasara ba tare da sun jawo asarar rai ko dukiya ba
- Bayanan sirri daga al’umma sun taimaka wajen gano barazanar da wuri, yayin da aka kara tsaurara sintirin jami’an tsaro domin kare matafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta samu nasarar gano tare da lalata wasu bama-bamai (IEDs) da ake zargin ’yan bindiga ne suka dasa a kan hanyar Kunchin Kalgo da ke karamar hukumar Tsafe.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Yazid Abubakar, ya bayyana wa manema labarai a daren Alhamis cewa lamarin ya faru ne ranar 13 ga Yuni, 2026, da misalin karfe 4:15 na yamma.

Source: Facebook
Yan sanda sun kwance bama-bamai
A cewarsa, jami’an Sashen Yaki da Manyan Laifuffuka (VCRU) tare da hadin gwiwar Sashen Kwance Bama-bamai (EOD) sun gudanar da aikin cikin nasara, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Ya ce:
“An gano tare da lalata wasu abubuwan fashewa da aka dasa cikin dabara domin haddasa mummunar asara ga matafiya da masu amfani da hanyar.”
Mazauna yankin sun bada hadin kai
DSP Yazid ya bayyana cewa nasarar ta samu ne sakamakon kyakkyawar alaka tsakanin jami’an tsaro da al’umma, kamar yadda Guardian ta ruwaito.
A cewarsa, rundunar ta samu sahihan bayanai cikin lokaci daga mazauna yankin, lamarin da ya bai wa jami’an damar daukar matakin gaggawa kafin wata illa ta faru.
Rundunar yan sandan Zamfara ta yabawa mazauna yankin bisa nuna kulawa da bayar da bayanan da suka taimaka wajen dakile barazanar.
Ta ce hadin kan jama’a na ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen nasarar ayyukan tsaro a fadin jihar Zamfara.

Kara karanta wannan
Bincike: 'Yan bindiga ne suka mika gawar Janar Rabe hannu da hannu? Gaskiya ta fito
Za a yi farautar masu hannu a lamarin
Rundunar ta tabbatar wa jama’a cewa tana ci gaba da kokarin gano tare da cafke wadanda ke da hannu wajen dasa bama-baman domin gurfanar da su a gaban kuliya.
Haka kuma ta bayyana cewa an kara tura jami’an tsaro a sassa daban-daban na jihar domin hana aukuwar makamantan hare-hare da kuma tabbatar da tsaron matafiya da mazauna yankuna.

Source: Twitter
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, Ahmad Muhammad Bello ya bukaci jama’a su ci gaba da sanya ido tare da kai rahoton duk wani abu da suka gani mai kama da barazana ga hukumomin tsaro.
Ya kuma tabbatar musu da cewa za a dauki matakin gaggawa kan duk wani sahihin bayani tare da kiyaye sirrin masu bayar da bayanan.
Bam ya tarwatse da matafiya a Zamfara
A wani labarin, kun ji cewa wani bam da aka dasa a kan hanya ya tarwatse a titin Anka zuwa Bagega a jihar Zamfara, inda mutum guda ya rasa ransa.

Kara karanta wannan
Bayan mutuwar Janar Rabe Abubakar, an ji halin da matarsa ke ciki a hannun 'yan bindiga
Lamarin ya faru ne da sanyin safiya lokacin da bam din ya tarwatse da wata motar haya kirar Golf-3 Wagon da ke dauke da fasinjoji daga kauyen Bagega zuwa garin Anka.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, ya tabbatar da aukuwar lamarin tare da bayyana cewa an tura jami’an tsaro zuwa wurin domin shawo kan matsalar.
Asali: Legit.ng
