Abu Ya Girma: 'Yan Bindiga Sun Kashe Fitaccen Dan Kasuwa a Jihar Katsina

Abu Ya Girma: 'Yan Bindiga Sun Kashe Fitaccen Dan Kasuwa a Jihar Katsina

  • 'Yan bindiga sun kashe fitaccen ɗan kasuwa kuma manomi, Alhaji Bala Sanin Kawo, bayan sun yi garkuwa da shi a jihar Katsina
  • Rahotanni sun nuna cewa iyalansa sun biya kuɗin fansa domin kubutar da shi kafin daga bisani a gano gawarsa
  • Marigayin ya kasance sanannen manomi kuma ɗan kasuwa a karamar hukumar Dandume da maƙwabtan yankuna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina, Nigeria - An shiga alhini a Jihar Katsina bayan rahotanni sun bayyana cewa wasu ’yan bindiga sun kashe fitaccen ɗan kasuwa kuma manomi, Bala Sanin Kawo.

Rahotanni sun nuna cewa yan ta'addan sun kashe mutumin ne kwanaki kaɗan bayan sun yi garkuwa da shi a ƙaramar hukumar Dandume ta jihar Katsina.

Gwamnan Katsina.
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Radda a wurin kaddamar da dakarun C-Watch Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Source: Facebook

Majiyoyi daga yankin sun shaidawa Premium Times cewa an sace Bala Sanin Kawo tare da ɗaya daga cikin ma’aikatansa a ranar Alhamis yayin da suke dawowa daga gonarsa da ke kusa da kauyen Dantakari.

Kara karanta wannan

Ana jimamin Janar Rabe, sarki ya sake mutuwa a hannun 'yan bindiga

Iyalan manomin sun biya kuɗin fansa

Bayan sace shi, rahotanni sun nuna cewa masu garkuwar sun tuntubi iyalansa tare da neman kuɗin fansa domin a sako shi.

Ko da yake ba a tabbatar da adadin kuɗin da aka nema ba, wasu rahotanni sun ce da farko an nemi kuɗaɗe masu yawa, amma daga baya aka buƙaci iyalansa su tara Naira miliyan biyar.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce iyalan mamacin sun tattara kuɗin tare da miƙa su kamar yadda masu garkuwar suka umarta amma bayan an kai kuɗin sai maharan suka fadi wurin da suka ajiye gawarsa.

“Bayan an kai kuɗin fansar, aka cewa iyalansa su je wani wuri. A can ne aka ce suka gano gawarsa,” in ji majiyar.

Har yanzu ba a san yadda ya mutu ba

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a tabbatar da yadda Alhaji Bala Sanin Kawo ya rasa ransa ba, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

Kara karanta wannan

Mataimakin kwamishinan 'yan sanda, Khan Salihu ya rasu bayan ya dawo daga masallaci

Marigayin ya kasance sanannen manomi kuma ɗan kasuwa a Dandume da maƙwabtan yankuna, inda aka san shi da manyan gonaki da kuma ɗaukar ma’aikata da dama.

Mutane da dama a yankin sun bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi ga al’umma.

Yan sanda.
Dakarun yan sandan Najeriya a cikin shirin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

’Yan sanda ba su tabbatar da lamarin ba

Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya ce zai bincika lamarin sannan ya bayar da bayani.

Sai dai har zuwa lokacin kammala wannan rahoto, rundunar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba.

Janar Rabe ya rasu a hannun yan bindiga

A wani labarin, kun ji cewa Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya), wanda yan bindiga suka yi garkuwa da shi tare da matarsa a jihar Katsina , ya rasa rayuwarsa.

Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da rasuwar tsohon Janar, wanda ya rasu yayin da yake tsare a hannun ‘yan bindiga.

Sanarwar ta ce duk da kokarin da gwamnatin jihar da hukumomin tsaro suka yi domin ganin an kubutar da shi cikin koshin lafiya, hakan bai samu ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262