Gwamna Makinde Ya Bayyana Wurin da Aka Boye Dalibai da Malaman da 'Yan Bindiga Suka Sace
- Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya ce dalibai da malaman da aka sace a Oriire suna cikin gandun dajin Old Oyo National Park
- Yau kwanaki 27 kenan da aka yi garkuwa da su daga makarantu uku a karamar hukumar Oriire ta jihar Oyo
- Makinde ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da duka wadand ak sace sun dawo lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Oyo, Nigeria - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya yi karin haske kan halin da dalibai da malamai da yan bindiga suka sace a Yawota da Ahoro-Esinle da ke karamar hukumar Oriire ke ciki.
Makinde ya bayyana cewa dalibai da malamansu da aka yi garkuwa da su daga makarantu uku, suna nan a cikin dajin Old Oyo National Park.

Kara karanta wannan
Tinubu zai kashe Naira tiriliyan 5 kan tsaro, za a dauki sababbin ƴan sanda 50000

Source: Facebook
Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa Gwamna Makinde ya bayyana hakan ne a cikin wasikar bayanansa ta mako-mako mai lamba ta 140 da aka fitar ranar Juma'a.
Jami'an tsaro na kokarin ceto su
A cewarsa, jami'an tsaro da gwamnatin Oyo na ci gaba da mayar da hankali kan yadda za a kubutar da wadanda aka sace cikin koshin lafiya.
Gwamnan ya tunatar da jama'a cewa kwanaki 27 sun shude tun bayan da aka sace daliban da malamansu daga makarantunsu, lamarin da ya jefa iyalansu da al'ummominsu cikin damuwa da rashin tabbas.
An sace mutane da dama ne a harin da aka kai makarantar Baptist Nursery and Primary School da ke Yawota, Community Grammar School da kuma L.A Primary School da ke Esiele a ranar 15 ga Mayun 2026.
Makinde ya amince cewa iyalan wadanda aka sace na fuskantar tsananin bakin ciki da fargaba, yana mai cewa ya fahimci cewa kalaman kwantar da hankali kadai ba za su iya rage radadin da suke ciki ba.
An gano wurin da daliban Oyo suke
Gwamnan ya ce rahotannin sirri da jami'an tsaro suka samu sun nuna cewa har yanzu wadanda aka sace suna cikin yankin gandun daji na Old Oyo National Park.
Ya bayyana cewa gandun dajin yana da matukar fadi, inda ya mamaye kusan kilomita 2,500 tare da ketare sassan kananan hukumomi goma na jihar Oyo.
Makinde ya ce girman yankin da wahalar shiga wasu sassa na dajin na daga cikin manyan kalubalen da jami'an tsaro ke fuskanta wajen gudanar da aikin ceto.

Source: Twitter
Gwamnatin Oyo ta kara zage damtse
A cewar gwamnan:
"Ana bin duk wata sahihiyar hanya ta bayanan sirri, kuma ana amfani da duk wata hanyar doka domin tabbatar da kubutar da wadanda aka sace cikin aminci."
Ya kara da cewa aikin ceto na bukatar hakuri, kyakkyawan tsari da kuma hadin kai tsakanin jami'an tsaro daban-daban domin cimma nasara, kamar yadda Leadership ta kawo.
Daliban Oyo: An fara zargin gwamnoni 6
A wani labarin, kun ji cewa kungiyar haɗin kan kabilar yarbawa ta AYDM ta zargi gwamnonin shiyyar Kudu maso Yamma da sakaci a harkar tsaron yankin.
Kungiyar ta yi ikirarin cewa sakacin da gwamnonin suka yi tun bayan fara kwararar yan ta'adda zuwa yankin, shi ne ya jawo sace dalibai a jihar Oyo.
AYDM ta yi ikirarin cewa gwamnonin suna da hannu da duk abubuwan da ke faruwa a yankin saboda gaza daukar matakan kariya tun farko.
Asali: Legit.ng

