Musulmar Afghaistan Aisha Wahab ta lashe zabe a Amurka
- Rahoto ya nuna cewa Aisha Wahab ta kafa tarihi bayan zama mutumiyar farko 'yar asalin Afghanistan da aka zaba a Majalisar Dokokin Amurka
- 'Yar siyasar ta jam'iyyar Democrat ta lashe zabe a California duk da makudan kudin da wasu kungiyoyi suka kashe wajen yakar takararta
- Wahab ta taba kafa tarihi bayan zama mace ta farko Musulma kuma 'yar asalin Afghanistan da aka zaba a Majalisar Dattawan jihar California
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
California, Amurka – Aisha Wahab, wata 'yar siyasar jam'iyyar Democrat, ta kafa tarihi bayan lashe zaben cike gurbin kujerar Majalisar Wakilan Amurka mai wakiltar mazaba ta 14 a jihar California.
Nasarar da ta samu ta sanya Wahab zama mutumiyar farko 'yar asalin Afghanistan da aka taba zaba a Majalisar Dokokin Amurka.

Source: Getty Images
Yahoo News ta wallafa cewa an bayyana nasarar Wahab a zaben na musamman da aka gudanar domin cike gurbin kujerar da tsohon dan majalisa, Eric Swalwell, ya bari.
Aisha Wahab ta lashe zabe
Aisha Wahab ta fuskanci gagarumar hamayya a lokacin yakin neman zabenta, inda kungiyoyin Super PAC suka kashe akalla dala miliyan 5 wajen yakar takararta.
Rahoton Politico ya nuna cewa wani bangare mai yawa na kudin da aka kashe wajen adawa da Wahab yana da alaka da kungiyar AIPAC da ke goyon bayan Isra'ila,.
An ce kungiyar ta kashe akalla dala miliyan 3 wajen tallafa wa babbar abokiyar hamayyar Wahab, Melissa Hernandez.
Duk da wannan matsin lamba, Wahab ta samu nasarar kayar da Hernandez a zaben da aka gudanar ranar Talata.
Kafin wannan zabe, Wahab ta riga ta yi fice a zaben fitar da gwani na watan Yuni, inda ta samu rata da ta haura maki 25 tsakaninta da Melissa Hernandez.

Kara karanta wannan
APC, ADC da jam'iyyun da suka bayyana shirinsu na fara yakin neman zaben shugaban kasa

Source: Getty Images
Wacece Aisha Wahab?
Wahab mamba ce ta jam'iyyar Democrat kuma ta riga ta kafa tarihi a fagen siyasar California kafin wannan sabon matsayi.
Ita ce mace Musulma ta farko kuma mutumiyar farko 'yar asalin Afghanistan da aka zaba a Majalisar Dattawan jihar California.
Nasararta a zaben Majalisar Wakilan Amurka ta kara tabbatar da tarihinta, yayin da aka samu karin damar shigar mata cikin manyan mukaman siyasa.
An samu damar neman kujerar ne bayan Eric Swalwell ya yi murabus daga majalisar a watan Afrilu sakamakon wasu zarge-zargen rashin da'a da suka shafe shi.
Duk da cewa Aisha Wahab ta lashe zaben na musamman, ita da Melissa Hernandez za su sake fafatawa domin samun cikakken wa'adin kujerar a zaben watan Nuwamba.
Bashin Amurka ya yi yawa
A wani labarin, mun ruwaito cewa jimillar bashin da ek bin gwamnatin Amurka ta haura dala tiriliyan 40 a karon farko a tarihin kasar..
Rahotanni sun nuna cewa wannan adadi ya karu ne bayan watanni biyar kacal da bashin kasar ya kai dala tiriliyan 39, yayin da kashe kudi ya karu,
Fadar White House ta ce gwamnatin shugaba Donald Trump na kokarin rage almubazzaranci da damfarar kudaden gwamnati tare da bunkasa tattalin arziki.
Asali: Legit.ng

