Mahaifi Ya Kona ’Yar Cikinsa saboda Malalar Fitsarin Kwance Kullum a Gadonsu
- Wani mutum mai suna Paul a Owo, Ondo, ya shiga hannun ‘yan sanda bayan zargin dukan ‘yarsa mai shekaru 10 kan fitsarin kwance
- Rahotanni sun ce mutumin ya danna mata ƙarfen guga mai zafi a sashen jikinta na sirri, lamarin da ya jawo mata munanan raunuka
- Kwamishinar Harkokin Mata ta Ondo ta ce yarinyar na karbar magani a FMC Owo, kuma za a yi mata wata tiyatar dashen fata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Owo, Ondo - An mika wani mutum mai suna Paul ga rundunar ‘yan sandan Ondo bisa zargin cin zarafin ‘yarsa mai shekaru 10 saboda fitsarin kwance.
An ce wanda ake zargin ya danna ƙarfen guga mai zafi a sashen jikinta na sirri, a Upemen da ke ƙaramar hukumar Owo.

Source: Original
Kwamishinar Harkokin Mata da Ci gaban Al’umma ta Ondo, Dr Seun Osamaye, ce ta bayyana hakan ranar Talata, bayan ziyarar da ta kai wa yarinyar a Federal Medical Centre, Owo.

Kara karanta wannan
Miyagun kwayoyi: Dubun tsohon shugaban ƙaramar hukuma ta cika, ya shiga hannu a Kano
Matakin da gwamnati ta dauka
Ta ce gwamnatin jihar ta dauki matakin gaggawa bayan samun rahoton lamarin, inda aka kama mahaifin tare da mika shi ga ‘yan sandan sashen Owo domin gurfanar da shi.
Osamaye ta ce gwamnatin Ondo karkashin jagorancin Gwamna Lucky Aiyedatiwa ta himmatu wajen kare yara da tabbatar da jin dadinsu a jihar.
Ta bayyana cewa yarinyar ta samu munanan raunuka bayan lamarin, kuma yanzu tana bukatar wata tiyata ta biyu da za ta kunshi dashen fata a FMC Owo.
Kwamishinar, wadda ta jagoranci tawagar ma’aikatar zuwa asibitin domin duba lafiyar yarinyar bayan tiyatar farko, ta ce gwamnati ta shiga lamarin domin tabbatar mata da ingantaccen magani da sauran tallafin da take bukata.
Ta yaba wa Gwamna Aiyedatiwa saboda saurin daukar mataki da kuma kulawarsa kan jin dadin yarinyar, tana mai cewa gwamnatin za ta ci gaba da ba da muhimmanci ga tsaro, mutunci da walwalar yara.

Kara karanta wannan
Saurayi ya yi jima'i da budurwa, ya fille mata wuya ta mutu ya sha jinin ta a otel
Daraktan Kiwon Lafiya na FMC Owo, Dr Adeyinka Aiyeyemi, ya yaba wa gwamnatin jihar saboda samar da yanayin da ya bai wa ma’aikatan lafiya damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Ya kuma ba da shawarar a samar wa iyayen yarinyar tallafin ilimin halayyar dan Adam, domin taimaka musu wajen fahimtar abubuwan da suka shafi lamarin.
Aiyeyemi ya sanar da kwamishinar cewa yarinyar za ta bukaci sake yin aikin dashen fata a matsayin wani bangare na ci gaba da jinyarta da murmurewa.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abayomi Jimoh, ya tabbatar da faruwar lamarin da kuma kama wanda ake zargin.
Ya ce bayan samun rahoton, jami’an bincike daga sashen ‘A’ na Owo sun gaggauta zuwa wurin, inda suka kama wanda ake zargin ba tare da bata lokaci ba.
Ya ce an tsare mutumin, yayin da aka mika shari’ar ga sashen kula da laifukan jinsi domin gudanar da bincike cikin sirri da daukar matakin da ya dace.
Yadda jabun magunguna ke hallaka mutane a Ondo
An ji cewa daraktan asibitin UNIMEDTH ya yi gargadin cewa jabun magunguna na zama babbar barazana ga lafiyar jama’a.
Farfesa Michael Gbala ya bayyana cewa amfani fa jabun magunguna na iya zama hadari ga mutane ciye da illar yan bindiga.
Ya buƙaci masu ruwa da tsaki su inganta hanyoyin saye, rarrabawa da sa ido kan magunguna domin kare marasa lafiya daga amfani da jabun magunguna.
Asali: Legit.ng
