2027: Sanatan APC Salihu Mustapha Ya Yi Watsi da Jam'iyyar, Ya Yi Murabus
- Sanata mai wakiltar Kwara ta Tsakiya, Saliu Mustapha, ya sanar da yin murabus daga jam'iyyar APC bayan makonni na tuntuba
- Mustapha ya ce ya yanke shawarar ficewa daga APC ne sakamakon wasu sababbin abubuwan da suka faru a cikin jam'iyyar a jihar Kwara
- Sanatan ya tabbatar wa al'ummar mazabarsa cewa sauya jam'iyyar siyasa ba zai sauya manufarsa da jajircewarsa wajen yi musu hidima ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Ilorin, Kwara – Sanata mai wakiltar mazabar Kwara ta Tsakiya, Saliu Mustapha, ya yi murabus daga jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya..
Mustapha ya bayyana matakin nasa ne a wata sanarwa da ya fitar, inda ya hada da takardar murabus mai kwanan wata 14 ga watan Agustan 2026.

Source: Facebook
Sanatan ya aika da takardar murabus din ne ga shugaban jam'iyyar APC na mazabar Gambari da ke karamar hukumar Ilorin ta Gabas a jihar Kwara kamar yadda ya wallafa a Facebook.
Dalilin fitarsa daga APC
Saliu Mustapha ya ce bai yanke shawarar ficewa daga jam'iyyar APC cikin gaggawa ba, domin ya dauki makonni yana tuntubar masu ruwa da tsaki.
Ya ce ya tattauna da magoya bayansa, al'ummar mazabar Kwara ta Tsakiya da kuma wasu fitattun mutanen jihar Kwara kafin daukar matakin.
Mustapha ya ce sababbin abubuwan da ke faruwa a cikin APC a jihar Kwara ne suka sanya shi sake nazari kan matsayinsa a jam'iyyar.
Punch ta wallafa cewa ya ce:
"Bayan yin nazari sosai kan abubuwan da ke faruwa a jam'iyyar a jihar Kwara, na yanke shawarar yin murabus daga kasancewata mamba a jam'iyyar a jihar."
Sanatan ya kara da cewa siyasa a ganinsa bai kamata ta kasance domib neman mulki kawai ba, ya ce ya kamata a gina ta kan karfafa mutane, ka'idoji da kuma wata manufa mai kyau.
Sanatan ya yi godiya ga Tinubu
Duk da ficewarsa daga jam'iyyar, Sanata Saliu Mustapha ya mika godiyarsa ga shugabannin APC karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Ya ce ya yaba da alakar da ya gina da kuma irin kwarewa da gogewar da ya samu a lokacin da yake mamba a jam'iyyar.
Mustapha, wanda aka zabe shi a matsayin sanata a karkashin inuwar APC, ya ce sauyin da ya yi na siyasa ba zai sauya manufarsa ta yi wa al'ummar Kwara ta Tsakiya hidima ba.

Source: Facebook
Ya tabbatar wa magoya bayansa, abokan siyasarsa da masu ruwa da tsaki cewa zai ci gaba da tsayawa kan ka'idoji da manufofin da ya yi imani da su.
Dan Ganduje ya koma APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa Abdulaziz Abdullahi Umar Ganduje ya koma jam'iyyar APC bayan ya fice daga cikinta a kwanakin baya.
Abdulaziz ya sanar da komawarsa APC ne a garinsu na Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano, bayan ya shafe wasu watanni a jam'iyyar NDC.
Komawarsa APC na zuwa ne bayan ya bayyana aniyarsa ta neman kujerar dan majalisar wakilai mai wakiltar Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado a babban zaben shekarar 2027.
Asali: Legit.ng

