Sheikh Daurawa Ya Magantu kan Muslim/Muslim, Ya Fadi Wanda Ya Kamata a Zaba
- Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ce siyasa ba addini ba ce, yana mai cewa bai kamata a hada rigingimun addini da siyasar Najeriya ba
- Malamin ya bayyana cewa ya kamata ’yan Najeriya su zabi shugabanni bisa kwarewa, ayyukan alheri da abin da suke tsammanin za su yi
- Daurawa ya ce tikitin Musulmi da Musulmi, Musulmi da Kirista ko Kirista da Kirista duk siyasa ce, don haka bai kamata a kafurta kowa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi magana game da rikicin siyasa da ya taso musamman kan tikitin Musulmi da Musulmi.
Sheikh Daurawa ya bayyana matsayarsa game da siyasar Najeriya da ya shafi tikitin Musulmi da Musulmi da na Kirista da Musulmi.

Source: Facebook
Babban malamin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo yayin hira da shafin DW Hausa wanda ta wallafa a shafin Facebook.
Daurawa ya ce siyasar Najeriya ba addini ba ne
Sheikh Daurawa ya ce siyasa ba addini ba ne saboda tsarin dimukradiyya bai da alaka da Musulunci bare a rika ta da jijiyoyin wuya.
Ya ce abin da ya kamata a yi a siyasa shi ne zaben domin kwarewa da ayyukan alheri na mutum ko kuma mai ake tsammanin zai yi idan aka zabe shi.
Daurawa ya ce:
"Shi yasa na ke fada maka ai, idan ka ce a yi kaza kaza to ka zama dan kaza kaza, mu kuma shi ne muna son siyasa din da gyara tunanin yan siyasa.
"Ba maganar waye za a zaba ba, me zai yi idan an zabe shi, idan maganar addini za a yi, to addini ake yi a Najeriya? ai dimukradiyya ba tsari ne na addini ba.
"A kundin tsarin mulki ma bai ma yadda akwai addini ba kwata-kwata ko na Kiristanci ko na Musulunci, idan aka ce tsarin Musulunci za a yi amfani da shi ai babu mai tsayawa takarar sai Musulmi."

Source: Facebook
'Babu bambanci tsakanin tikitin takara' - Daurawa
Shiekh Daurawa ya ce da tikitin Musulmi da Musulmi da Musulmi da Kirista da kuma na Kirista da Kirista duk abi daya ne a siyasar Najeriya.
Ya ce bai kamata a rika saka rigingimun addini a cikin siyasa ba wurin zagi ko kafurta wani kawai saboda bambancin ra'ayi na siyasa saboda babu jam'iyyar Musulunci ko ta Kiristanci.
"Idan Musulmi da Musulmi suka tsaya taraka ko Musulmi da Kirista ko Kirista da Kirista duk abu daya ne, duk siyasace, saboda babu wanda zaka cire domin a zabi wani.
"Ida muka dauko rigingimun addini muka saka a harkar siyasa, ka zagi wancan ka kafurta wancan, to wace jam'iyya ce ta Musulunci wacece ta ke taiya kan tsarin Musulunci ko Kiristanci.
"Wanda ya ce a yi Muslim/Musulmi a waje na bai yi laifi ba, haka nan wanda ya ce a yi Kirista da Musulmi ko Kirista da Kirista duk ba su yi laifi ba."
- Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Matashi ya kare kalaman Jingir kan Muslim/Muslim
Mun ba ku labarin cewa matashin ɗan siyasa Khamis Musa Darazo ya soki masu zagin Sheikh Sani Yahaya Jingir, yana mai cewa irin wannan hali rashin tarbiyya ne.
Darazo ya ce bai kare Sheikh Jingir ba saboda goyon bayan gwamnatin Tinubu kawai, sai dai ya yi Allah wadai da cin mutuncinsa.
Ya bayyana cewa malamin na da ’yancin bayyana ra’ayinsa, tare da yi masa addu’ar Allah Ya ƙara masa lafiya, daraja da tsawon rai.
Asali: Legit.ng


