Abin da Zababben Gwamnan Osun Ya Fadawa Tinubu Gaba da Gaba a Fadar Shugaban Kasa
- Shugaba Bola Tinubu ya karɓi bakuncin gwamnan Osun, Ademola Adeleke, a Fadar Shugaban Ƙasa bayan ya sake lashe zaɓen gwamna
- Adeleke ya kai wa Tinubu takardar shaidar nasara tare da gode masa kan yadda ya ba da damar gudanar da zaɓen cikin ’yanci da adalci
- Tinubu ya buƙaci Adeleke ya yi amfani da sabon wa’adinsa wajen ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya da ci gaban Jihar Osun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya karɓi bakuncin Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Alhamis, 19 ga Agusta, 2026.
Gwamna Adeleke ya kai wa Bola Tinubu ziyara ne domin ya gabatar masa da takardar shaidar nasara bayan ya sake lashe zaɓen gwamnan Osun a karo na biyu.

Source: Twitter
Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa Adeleke ya isa Fadar Shugaban Ƙasa da misalin ƙarfe 5:20 na yamma, inda ya gana da Shugaban Ƙasa a sirrance.
Hakam na zuwa ne kwanaki kadam bayan ya karɓi takardar shaidar nasara daga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).
Adeleke, wanda ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar Accord, ya samu ƙuri’a 511,067, inda ya doke ɗan takarar jam’iyyar APC, Bola Oyebamiji, wanda ya samu ƙuri’a 444,815.
Gwamna Adeleke ya gode wa Tinubu
Da yake magana bayan ganawar da suka yi, gwamnan ya ce ya ziyarci Tinubu ne domin nuna godiya gare shi kan rawar da ya taka wajen tabbatar da abin da ya bayyana a matsayin zaɓe cikin ’yanci da adalci.
“Na zo nan ne domin gode wa Mai Girma Shugaban Ƙasa, uban ƙasa, saboda ya yi gwagwarmaya domin wannan dimokuraɗiyya. Shi ya sa ya ba da damar gudanar da zaɓe cikin ’yanci da adalci,” in ji Adeleke.
Ya ce sakamakon zaɓen ya nuna cewa muradin jama’a na iya yin nasara idan aka bar tsarin dimokuraɗiyya ya yi aiki yadda ya kamata.
Tinubu ya ba Adeleke shawara
A nasa jawabin, Shugaba Tinubu ya buƙaci Adeleke ya yi amfani da sabon wa’adin da jama’a suka ba shi wajen inganta haɗin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Shugaban Ƙasar ya kuma gargadi gwamnan da kada ya mayar da ’yan adawar siyasa saniyar ware ko ya gallaza musu, yana mai jaddada cewa lashe zaɓe ba yana nufin an ci abokan hamayya da yaƙi ba.

Source: Twitter
Tinubu ya buƙaci Adeleke ya mayar da hankali kan shugabanci da inganta ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya da sauran fannoni da suka shafi rayuwar mazauna jihar.
Ya kuma shawarci gwamnan da ya guji manufofin da ka iya raunana ƙarfin jihar na biyan albashi da hakkokin fansho, kamar yadda Vanguard ta kawo.
An faramkai ayarin Gwamna Adeleke
A wani rahoton, kun ji cewa wasu da ake zargin ’yan daba ne sun kai hari kan tawagar Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun bayan ya kammala ziyarar fadar Ataoja na Osogbo.
Rahotanni sun nuna cewa an yi musayar harbe-harbe tsakanin jami’an tsaron gwamnan da maharan na tsawon kusan mintuna 12 zuwa 15.
Asali: Legit.ng

