Abin da Gwamnoni 36 Suka Bukaci a Yi kafin Kafa Rundunar Yan Sandan Jihohi a Najeriya

Abin da Gwamnoni 36 Suka Bukaci a Yi kafin Kafa Rundunar Yan Sandan Jihohi a Najeriya

  • Gwamnonin jihohi 36 sun sake bayyana cikakken goyon bayansu ga kafa ’yan sandan jihohi domin yakar matsalar tsaro da ke kara tabarbarewa a Najeriya
  • A wani taro da suka gudanar, gwamnonin sun ce dole kafa sabuwar rundunar ta kasance bisa tanadin kundin tsarin mulki da kare hakkokin ’yan kasa
  • Sun kuma tattauna kan muhimman batutuwa a taron ciki har da gyaran kundin tsarin mulki da tsarin aiwatar da ’yan sandan jihohi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnonin jihohi 36 na Najeriya karkashin kungiyarsu ta NGF sun sake bayyana goyon bayansu ga kafa rundunar ’yan sandan jihohi.

Gwamnonin sun bukaci a tabbatar da cewa rundunar yan sandan jihohin da za a kafa ta yi daidai da kundin tsarin mulki, tsarin tarayya da kuma kare hakkokin ’yan kasa.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa sun gano abin da ke kullawa domin sauke manyan hafsoshin tsaron Najeriya

Gwamnoni.
Gwamnonin jihohin Najeriya yayin da suke tsakiyar taro a Abuja Hoto: @NGFSecretariat
Source: Facebook

Matsayar ta fito ne bayan kammala taronsu na biyu da aka gudanar a Abuja daga ranar Laraba zuwa safiyar Alhamis, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar bayan taron da shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya sanya wa hannu tare da sauran gwamnonin.

Gwamnonin jihohi 6 sun karbi bayanai

Sanarwar ta bayyana cewa gwamnonin sun karbi bayanai daga sakatariyar NGF da kuma tawagar manyan lauyoyin gwamnati na jihohi kan kokarin kafa ’yan sandan jihohi a Najeriya.

Gwamnonin sun ce an gudanar da wata ganawa ta musamman da manyan lauyoyin jihohi domin nazarin gyare-gyaren kundin tsarin mulki da kuma tsarin da za a bi wajen kafa rundunar.

Tun a watan Afrilu ne kungiyar gwamnonin ta amince da fara shirya tsarin ’yan sandan jihohi domin dacewa da gyaran kundin tsarin mulki da ake shirin yi.

Tsarin ya kunshi muhimman abubuwa da suka hada da tsarin shugabanci, hanyoyin samar da kudade, ka’idojin daukar ma’aikata, tsarin zamani na fasaha da kuma hanyoyin sa ido.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi, shugabannin Kirista sun yi kira da murya daya kan matsalar tsaro

Gwamnan Kwara.
Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq Hoto: @AARahman
Source: Twitter

NGF ta sanya sharadin kafa yan sandan

Da yake karanta sanarwar bayan taron, gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya ce gwamnonin sun jaddada muhimmancin samar da rundunar ’yan sandan jihohi da za ta yi daidai da tsarin tarayyar Najeriya da kuma kare hakkokin jama'a.

"Gwamnonin sun jaddada bukatar kafa ’yan sandan jihohi cikin tsarin da ya dace da kundin tsarin mulki, tsarin tarayya da kuma kare hakkokin ’yan kasa," in ji sanarwar.

Ya kara da cewa hadin gwiwar da aka samu tsakanin jihohi da manyan lauyoyi zai taimaka wajen karfafa matsayar jihohin baki daya kan wannan batu, cewar rahoton This Day.

Majalisa ta amince da kudirin yan sandan jihohi

A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar wakilan Najeriya ta amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da zai bai wa jihohi damar kafa rundunar ‘yan sandan jihohi a Najeriya.

An gudanar da kada kuri’ar ne ta hanyar daga hannu, inda kusan ‘yan majalisa 288 suka goyi bayan kudirin yayin da mutum hudu kacal suka nuna adawa da shi.

Kudirin na neman sauya tsarin aikin ‘yan sanda a Najeriya ta hanyar kafa rundunar ‘yan sandan tarayya da kuma ta jihohi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262