Makonni da Sace Dalibai a Borno, Boko Haram Ta Babbake Makarantu a Chibok

Makonni da Sace Dalibai a Borno, Boko Haram Ta Babbake Makarantu a Chibok

  • Jama'a a jihar Borno sun fada cikin sabon tashin hankali bayan wani mummunan hari da ake zargin mayakan Boko Haram/ISWAP sun kai
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kai hari inda suka ƙona makarantu biyu a ƙauyen Kautikari da ke ƙaramar hukumar Chibok a Borno
  • Maharan sun kai harin ne da yammacin ranar Asabar, lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin tserewa zuwa cikin daji domin tsira

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Borno - Wasu da ake zargin mayakan ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP ne sun ƙone makarantar firamare da makarantar sakandare a ƙauyen Kautikari da ke ƙaramar hukumar Chibok a jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai farmaki ƙauyen da 7:00 na yammacin ranar Asabar, inda suka haddasa tashin hankali a yankin.

Kara karanta wannan

'Ba makaranta ba ce,' An samu sababbin bayanai kan harin Boko Haram a Borno

Boko Haram ta sake kai hari Borno
Taswirar jihar Borno inda ƴan Boko Haram suka ƙona makarantu Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daily Trust ta wallafa cewa lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake ci gaba da fargaba kan makomar ɗaliban makarantar Mussa Primary da Junior Secondary School da ke Askira-Uba.

An sace dalibai daga makarantu biyu aka kusan wata guda da ya gabata kuma kawo wannan lokacin, babu su ko labarin halin da suke ciki.

Wasu mazauna Borno sun tsere zuwa dawa

Daily Post ta ruwaito cewa majiyoyin tsaro sun bayyana cewa duk da harin, babu rahoton rasa rai ko jikkatawa a lokacin da aka kai farmakin.

Sai dai mazauna yankin sun yi gaggawar tserewa zuwa cikin dazuka domin neman mafaka da kare rayukansu daga barazanar maharan.

Wani mazaunin yankin ya ce wannan ba shi ne karo na farko da maharan suka kai hari ƙauyen ba, amma ya bayyana mamakinsa kan yadda suka mayar da hankali wajen ƙona makarantu a wannan karon.

A cewarsa, a hare-haren da suka gabata, maharan sun kai farmaki yankin ba tare da lalata kadarorin gwamnati ko na jama'a ba.

Kara karanta wannan

Dalibai sun tsere, iyaye sun kidime bayan jita jitar yan bindiga sun kutsa makarantu a Neja

Yadda mazauna Borno suka shiga ruɗani

Mazaunin ya bayyana cewa ƙona makarantar firamare da kuma makarantar sakandaren yini wani sabon salo ne da ba a saba gani daga irin waɗannan hare-hare a yankin ba

Jama'a sun tsere daga gidajensu a jihar Borno
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum Hoto: The Governor of Borno State
Source: Facebook

Ya ƙara da cewa hakan ya jefa al'umma cikin damuwa, musamman duba da muhimmancin cibiyoyin ilimi ga ci gaban yankin da makomar yara

Kawo wannan lokacin, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso bai fitar da sanarwar a kan harin ba.

Kyaftin Abdullahi Bakoji mai ritaya, tsohon jami'in soji kuma mai sharhi a kan harkokin tsaro ya shaida wa Legit cewa rashin tsaro a kasar nan ya kai matakin zama abin kunya.

Ya bayyana cewa:

""Wannan lamari, ya kamata ya zama babban abin nazari ga gwamnati da jami'an tsaro, a sake nazari kan dabarun da ake amfani da su a ƙasar nan."

Ya kara da cewa akwai buƙatar a sake duba tsarin da ake bi wajen tattara bayanan tsaro da dakile harin kafin a kai ga aikata shi.

Kara karanta wannan

Sace dalibai: Gwamna ya umarci rufe makarantu bayan samun rahoton DSS

Sojoji sun ƙwato ɗalibai daga Boko Haram

A wani labarin, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar ceto mutanen da 'yan ta'addan Boko Haram suka yi garkuwa da su a jihar Borno da ke Arewa maso Gabas.

Sojojin sun samu nasarar ceto mutanen ne bayan da 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su a garin Ngoshe da ke karamar hukumar Gwoza yayin da iyalansu suka shiga tashin hankali.

Dakarun sojojin sun bayar da kulawa ga mutanen da aka ceto ta hanyar duba lafiyarsu, kafin mika su ga iyalansu da suka dade cikin jimamin rashinsu da addu'ar gwamnatin ta ceto su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng