Okorocha Ya Hada APC, Gwamna da INEC Ya Maka a Kotu kan Takarar Sanata
- Rochas Okorocha ya buƙaci kotun tarayya ta tilasta wa INEC amincewa da shi a matsayin ingantaccen ɗan takara
- Ɗan Okorocha ya bayyana cewa mahaifinsa ne ya sami ƙuri'u mafi yawa wajen neman takarar sanatan Imo ta yamma
- Wallafa sunan Hope Uzodimma ta tayar da muhawara kan tsarin mulki wanda ya haramta wa gwamna riƙe wani muƙami
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Imo - Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha ya yi karar hukumar INEC saboda ba Gwamna Hope Uzodinma takarar sanata.
INEC ta wallafa sunan Mai girma Hope Uzodinma a matsayin wanda zai yi wa APC takarar sanata a Yammacin Imo a zabe mai zuwa.

Source: Facebook
Rochas Okorocha ya shigar da kara a kotu
Ranar Alhamis NAN ta rahoto cewa a dalilin takarar sanatan, Rochas Okorocha ya shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1854/2026 a kotu.
O.J. Aboje ya shigar da karar a babban kotun tarayya da ke Abuja, yana kalubalantar hukumar zabe, jam’iyyarsa ta APC da gwamnan Imo.
Rudani a Imo kan 'dan takaran sanatan APC
Okorocha ya sha kashi hannun abokin kararsa da ya nemi tikiti a zaben tsaida gwani. An ce gwamnan Imo ya yi nasara da kuri’u 230,464.
‘Dan Okorocha ya yi ikirarin mahaifinsa ya ci zaben APC da kuri’a 150, 780, sai gwamna ya zo na biyu da kuri’u 102, 158 a takarar tsaida gwani.
Lamarin ya zo da rudani domin an rasa wace kujera ‘dan takaran kuma gwamna mai-ci zai rike a badi domin sai a Junairun 2028 zai sauka.
The Cable ta ce za a kaddamar da Majalisa ta 11 a Yunin 2027 - lokacin wa’adin Uzodinma na gwamna bai kare ba, saura watanni shida.
Karar da lauyan Okorocha ya shigar
Lauyan da ya yi kara ya roki kotu ta duba ko INEC tana da hurumin sa ido a zaben tsaida gwanin sanatan Imo ta yamma na jam'iyyar APC.
Yana mai dogara da sashe na 183 na kundin tsarin mulki, Okorocha yana son jin ko ba Uzodinma takara bai saba wa doka da ka’ida ba.

Kara karanta wannan
Bayan shan kashi a Osun, shugaban matasan APC ya ba jam'iyyar mafita kan zaben 2027
Dokar Najeriya ta ce gwamnan jiha ba zai iya rike mukami na zartarwa ko a same shi da wani aikin albashi a lokacin da yake cikin ofis ba.
Aboje Esq. ya ce INEC ta saba wa dokar kasa da ta wallafa sunan Uzodinma a matsayin ‘dan takara alhali bai yi nasara a zaben gwani ba.

Source: UGC
Sanata Okorocha ya ce shi ne 'dan takara
Okorocha mai neman mulkin Najeriya yana so a watsar da wannan mataki sannan a ayyana shi tare da wallafa sunansa a matsayin ‘dan takara.
Idan ya yi nasara a karar, kotu za ta hana Uzodinma ko kuma wani da sunan APC bayyana shi a matsayin mai takaran sanata a zaben 2027.
Gwamnan Imo zai nemi ya koma majalisa
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya bayyana aniyarsa ta takarar kujerar Sanatan Imo ta Yamma a zaben 2027 kamar yadda aka ji labari.
Ana cewa gwamnan yana shirin murabus daga mukaminsa na gwamna domin ya dare kan wannan kujera ta Majalisar dattawa a shekarar badi.
Wasu rahotanni na nuni da cewa gwamnonin jam'iyyar APC na goyon bayan wannan mataki domin ganin ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.
Asali: Legit.ng
