Masu Garkuwa Da Mutane
Ba bu shakku dangane yadda lamarin tsaro ke ci gaba da dagulewa a kasar nan ba bu dare ba bu rana, ta'addanci musamman garkuwa da mutane ya yi kamari wajen addabar al'umma cikin wasu jihohi a Kudu da Arewacin Najeriya.
Jama’a wani kauyen jahar Katsina, Dallawar Mahauta sun fusata sakamakon yawaitan ayyukan yan bindiga masu garkuwa da mutane a yankinsu, a wannan lokaci sun dauki mataki da kansu inda suka yi halaka wasu barayin mutane guda uku.
A hirar da mahaifin sumayya yayi da majiyarmu, ya bayyana cewa iyalansa da danginsa gaba daya sun shiga mawuyacin hali tun bayan sace Sumayya, inda ya tabbatar da tana dauke da juna a biyu a lokacin da suka yi garkuwa da ita.
Majiyar Legit.com ta ruwaito daga cikin mutane goma sha biyu da aka kashe akwai mutane biyar yan gida daya da harin ya rutsa dasu yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa filin sauka da tashin jiragen jahar Sao Paulo, inji hakimin gar
Mun samu rahoton cewa a makon da ya gabata 'yan ta'adda da ake zargin Makiyaya ne na Fulani, sun yi garkuwa da wasu Fasinjoji shida akan hanyarsu ta garin Akunnu daka karkashin karamar hukumar Akoko ta jihar Ondo.
Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, masu garkuwa da Mutane sun yi awon gaba da wani Manomi mai shekaru 59 a duniya, Shugaba Garba, a kauyen Tudun Koya dake karkashin karamar hukumar Billiri ta jihar Gombe.
Majiyar Legit.com ta ruwaito kaakakin kwalejin, Adewale Oyekanmi ne ya sanar da haka cikin hirar da tayi da shi a garin Osogbo, inda yace baya gas ace ma’aikatan su takwas, yan bindigan sun halaka wani daga cikinsu dake kokarin ts
Rundunar Yansandan jahar Osun ta yi ram da wani Limamin Masallaci da abokansa guda uku da laifin satar wani mutum, Victor Akinbile tare da kasheshi ba tare da wani hakki ba, sai dai kawai don ya kasa biyansu naira miliyan uku kudi
A halin yanzu diyar shugaban jam'iyyar PDP na karamar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina, Zainaba Hussaini, ta shiga hannun 'yan ta'adda masu garkuwa da mutane yayin da suka yi awon gaba da ita a daren jiya na Laraba.
Masu Garkuwa Da Mutane
Samu kari