An bindige mutane 5 yan gida daya a wani hari da miyagu suka kaima banki

An bindige mutane 5 yan gida daya a wani hari da miyagu suka kaima banki

Akalla mutane goma sha biyu ne aka kashe yayin da wasu gungun yan bindiga suka kai farmaki a wasu bankuna dake garin Milagres na yankin Arewa maso gabashin kasar Brazil kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Majiyar Legit.com ta ruwaito daga cikin mutane goma sha biyu da aka kashe akwai mutane biyar yan gida daya da harin ya rutsa dasu yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa filin sauka da tashin jiragen jahar Sao Paulo, inji hakimin garin Lielson Landim.

KU KARANTA: Karshen duniya: Dalibin makaranta ya sassara abokinsa da gatari har lahira

Sakataren jahar Ceara, Andre Costa ya bayyana cewa an kaddamar da bincike game da harin don gano dukkanin masu hannu cikin lamarin, sai dai yace binciken farko farko da suka gudanar ya nuna cewa yan fashin ne suka kashe mutanen da suka yi garkuwa dasu, yayin da Yansanda suka kashe yan fashin.

“Wasu gagga gaggan miyagun mutane sun far ma garin Milagres da sanyin safiyar Juma’a inda suka garzaya wasu bankuna biyu da nufin yi musu fashi, daga nan ne aka yi musayar wuta tsakaninu da Yansanda.

“A wannan musayar wutan ne Yansanda suka kashe yan fashi guda shida, yayin da yan fashin suka kashe mutane shida da suka yi garkuwa dasu, amma Yansanda sun kama mutane biyu daga cikin yan fashin, haka zalika sun gano bamabamai da makamai da motoci guda uku.” Inji shi.

Wata majiya ta kara da cewa yan bindigan sun yi amfani da wata babbar motace wajen rufe hanayar da iyalan yan gida daya suke kai, da haka ne suka kamasu, kuma suka kashesu a daidai lokacin Yansanda suka bayyana a inda suke fashin.

“Ban taba ganin tashin hankali kamar wannan ba, inda cikin gidana a tsorace ina jin kukan mutanen da kuma karan harbe harbe.” Inji wata makwabciyar bankunan, Mendoca de Santa Helena.

Wannan lamari ya tayar da hankulan mazauna garin, wanda hakan yasa hukumar garin dakatar da wasu aikace aikacenta, tare da umartar dukkanin mazauna garin dasu yi zamansu a cikin gida har sai hankali ya kwanta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel