Makiyaya sun karbi fansar N2.2m kudin garkuwa a hannun ma'aikatan Kastam da NDLEA

Makiyaya sun karbi fansar N2.2m kudin garkuwa a hannun ma'aikatan Kastam da NDLEA

Za ku ji cewa a makon da ya gabata 'yan ta'adda da ake zargin Makiyaya ne na Fulani, sun yi garkuwa da wasu Fasinjoji shida akan hanyarsu ta garin Akunnu daka karkashin karamar hukumar Akoko ta jihar Ondo.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Fasinjoji yayin balaguro da misalin karfe 9.00 na safiya daga jihar Legas dauke cikin wata Motar haya kirar Sienna, sun yi gamo da wannan muguwar ta'ada ta garkuwa a ranar Talatar da ta gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa, tsautsayi da ba ya wuce ranarsa ya afkawa wannan Mutane da misalin karfe 1.00 na ranar Talatar inda 'yan ta'adda suka datse hanyarsu rike da makamai na Bindigu.

Makiyaya sun karbi fansar N2.2m kudin garkuwa da ma'aikatan Kastam da NDLEA
Makiyaya sun karbi fansar N2.2m kudin garkuwa da ma'aikatan Kastam da NDLEA
Asali: Twitter

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Makiyaya sun kada Mutanen da suka yi garkuwa da su cikin dokar Daji tamkar yadda suke kada Shanu, inda suka tsare su har na tsawon kwanaki biyar.

Cikin wadanda wannan tsautsayi ya afkawa sun hadar da; jami'ai na hukumar Kastam da kuma na hukumar yaki da ta'ammali da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA.

Baya ga shan mugun duka, 'yan ta'addan sun kuma nemi fansar Naira Miliyan biyar ta Mutane shidan da suka yi garkuwa da su, inda bayan sun samu nasarar dafe Naira Miliyan 2.2 suka suka bayar da 'yancin su a ranar Lahadin da ta gabata.

KARANTA KUMA: Ku kadawa shugaba Buhari kuri'un ku a Zaben 2019 - Gwamna Akeredolu ga masu ribatar shirin N-Power

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar Ondo, Femi Joseph, ya tabbatar da wannan lamari yayin ganawarsa da manema labarai cikin birnin Akure a ranar da ta gabata.

Kazalika jaridar Legit.ng cikin wani rahoton mai nasaba da wannan ta ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kutsa cikin wata Makarantar gaba da Sakandire a jihar Osun, inda suka yi awon gaba da Malamai biyar tare da batar da guda daya daga doron kasa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel