Kotu Ta Yi Hukunci Za a Rataye Jagoran Dabar Yan Bindiga Jibrin Halilu har Lahira
- Babbar Kotun Jihar Kogi ta yanke wa wani kasurgumin dan garkuwa da mutane, Jibrin Halilu hukuncin kisa ta hanyar rataya
- Kotun ta yanke wa dan bindigar wannan hukunci ne bayan an same shi da laifin garkuwa da makwabcinsa tare da kashe shi
- Rahoto ya tabbatar da cewa Iyalan mamacin sun biya Naira miliyan 2.5 a matsayin kudin kafin daga bisani aka kashe shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kogi, Nigeria - Babbar Kotun Jihar Kogi ta yanke wa wani jagoran dabar yan bindiga masu garkuwa da mutane, Jibrin Halilu hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan ta same shi da laifin yin garkuwa da makwabcinsa tare da kashe shi duk da karbar Naira miliyan 2.5 a matsayin kudin fansa daga iyalansa.

Kara karanta wannan
N70000 ta yi kadan: NLC za ta sake zama da Tinubu kan sabon mafi karancin albashi

Source: Getty Images
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa mai shari'a Abdul Awulu ne ya yanke hukuncin, inda ya samu Halilu da laifuffuka biyu na hada baki da kuma garkuwa da mutane.
Alkalin ya bayyana cewa laifuffukan sun saba wa sashe na 12, 6(1) da 4(3)(a) na Dokar Hana Garkuwa da Mutane da Sauran Laifuffuka Masu Alaka ta Jihar Kogi ta shekarar 2023.
Yadda aka yi garkuwa da mamacin
Hukumar tsaron farin kaya (DSS), wadda ta gurfanar da wanda ake tuhuma, ta shaida wa kotu cewa Halilu da sauran mambobin kungiyarsa sun yi garkuwa da Uche Offo, mamallakin otal sin Ever Ready da ke Angwa-Tiv a Obajana, ranar 23 ga Maris, 2023.
An bayyana cewa masu garkuwar sun bukaci kudin fansa, inda iyalan Offo suka biya Naira miliyan 2.5 domin a sako shi. Amma bayan sun karɓi kudin, daga bisani suka kashe shi.
An kashe wanda ya gane Jibrin Halilu
Wata majiya daga DSS ta bayyana cewa Offo ya gane Halilu a lokacin da yake tsare a hannun masu garkuwar, kasancewar makwabcinsa ne.
Majiyar ta ce ana zargin wannan ne ya sa aka kashe shi domin kada ya fallasa wanda ya yi garkuwa da shi, kamar yadda Daily Post ta rahoto.
Binciken jami'an tsaro ya kuma danganta Halilu da wani harin garkuwa da mutane da aka kai wa wani bawan Allah, Ibrahim Abdullahi a yankin Oshokoshoko da ke Lokoja ranar 2 ga Afrilu, 2023.

Source: Original
A cewar masu bincike, kungiyar da yake jagoranta ta karbi Naira miliyan 5 daga iyalan Abdullahi kafin daga bisani ta sake shi.
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan ta gamsu da hujjojin da masu gabatar da kara suka gabatar kan laifuffukan da ake tuhumar Halilu da aikatawa.
Kotu ta yanke wa Hauwa'u hukuncin kisa
A wani rahoton, kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke jihar Katsina ta yankewa Hauwa’u Mukhtar hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifin ta’addanci.
Mai shari’a A.B. Bawale ne ya yanke hukuncin bayan kotun ta tabbatar da cewa an same ta da laifin hada baki da kuma taimaka wa ayyukan ‘yan ta’adda.
Bayanan kotu sun nuna cewa jami’an DSS sun kama Hauwa’u Mukhtar ne ranar 16 ga watan Satumban 2023 a tashar mota ta Jibia da ke jihar Katsina.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
