Babbar Magana: An yi garkuwa da wani Manomi a jihar Gombe

Babbar Magana: An yi garkuwa da wani Manomi a jihar Gombe

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, masu garkuwa da Mutane sun yi awon gaba da wani Manomi mai shekaru 59 a duniya, Shugaba Garba, a kauyen Tudun Koya dake karkashin karamar hukumar Billiri ta jihar Gombe.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Mista Muhammadu Mukaddas, shine ya bayar da shaidar wannan rahoto yayin ganawarsa da manema labarai cikin Birnin Gombe a ranar Talatar da ta gabata.

Mista Mukaddas ya bayyana cewa, hukumar sa ta dukufa wajen tabbatar da bincike na diddigi kan wannan lamari da tun a ranar Litinin din da ta gabata ya garzaya farfajiyar da wannan ta'addanci ya auku domin ganewa idanunsa.

Babbar Magana: An yi garkuwa da wani Manomi a jihar Gombe

Babbar Magana: An yi garkuwa da wani Manomi a jihar Gombe
Source: Twitter

Ya ci gaba da cewa, kawowa yanzu ba bu wasu ababen zargi da suka shiga hannu illa iyaka shimfidar matakai da suka malala da za ta kai su ga cafke masu hannu cikin wannan muguwar ta'ada.

KARANTA KUMA: Ma su cewa Shugaba Buhari ya mutu sun susuce - Osinbajo

Kwamishinan ya kuma nemi hadin kai daga bangaren al'umma wajen tallafawa jami'ai da rahotanni ma su riba ta fuskar tabbatar da tsaro gami da zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali a fadin jihar.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa, a halin yanzu wadanda suka yi garkuwa da Dattijon sun bukaci makudan kudin fansa na Naira miliya 30 yayin da suka tuntubi wani amininsa, Alhaji Abubakar Bappa, da ya kasance daya daga cikin manema tikitin takarar kujerar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar adawa ta PDP.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel