Da dumi dumi: Gungun masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da ma’aikata 8

Da dumi dumi: Gungun masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da ma’aikata 8

Gungun yan bindiga sun yi awon gaba da wasu ma’aikatan kwalejin kimiyya na da jahar Osun dake garin Esa-Oke a ranar Talata 4 ga watan Disamba kamar yadda rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN, ta bayyana.

Majiyar Legit.com ta ruwaito kaakakin kwalejin, Adewale Oyekanmi ne ya sanar da haka cikin hirar da tayi da shi a garin Osogbo, inda yace baya gas ace ma’aikatan su takwas, yan bindigan sun halaka wani daga cikinsu dake kokarin tserewa.

KU KARANTA:Kaico! Yan bindiga sun bindige jami’an Yansanda 16 a jahar Zamfara, 20 sun ɓace

A cewar Kaakakin, lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:30 na ranar Talata, yayin da yan bindigan suka tare hanyar Esa-Oke suka tare motoci da dama, daga ciki har da ma’aikatan makarantar, sa’annan suka yi awon gaba dasu.

“Yan bindigan basu tuntubi iyalan ma’aikatan ba ko kuma hukumar makarantar ba har zuwa yanzu yan, amma jami’an rundunar tsaro ta sirri, DSS, da na kungiyar matsafan OPC sun shiga farautarsu a dazukan yankin don ceto ma’aikatan.” Inji Kaakaki.

Itama Kaakakin rundunar Yansandan jahar Osun, Folashade Odoro ya bayyana cewa Yansanda na sane da lamarin, kuma zasu gabatar da jawabi a hukumance nan bada jimawa ba.

Wannan ne karo na biyu a cikin shekarar 2018 da masu garkuwa da mutane suke yin awon gaba da mutane a jahar, inda a watan Yuni suka saci wani babban limamin Coci da abokansa guda biyu akan hanyar Iwo-Osogbo.

A wani labarin kuma rundunar Yansandan jahar Zamfara ta tabbatar da kashe jami’anta guda goma sha shida (16) da tace yan bindiga da suka addabi jahar Zamfara ne suka kashesu, kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Majiyar Legit.com ta ruwaito rundunar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwar data fitar a ranar Talata 4 ga watan Disamba, inda tace an kashe Yansandan ne a wata artabu da aka kwasa tsakanin Yansanda da wasu gungun yan bindiga.

A ranar 29 ga watan Nuwamba ne yan bindigan suka yi ma ayarin motocin Yansanda kwantan bauna a garin Binin Magaji dake cikin karamar hukumar Zurmi ta jahar Zamfara da misalin karfe 4 na rana, sai dai a wancan lokacin rundunar cewa ta yi Dansanda daya aka kashe, sai a yanzu ne gaskiyar ta bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel