Roko na Musamman da Sarki Sanusi II Ya Yi ga Kungiyar EU game da Kano

Roko na Musamman da Sarki Sanusi II Ya Yi ga Kungiyar EU game da Kano

  • Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya tura bukata ta musamman ga kungiyar Tarayyar Turai game da halin da jihar ke ciki
  • Sanusi II ya jaddada muhimmancin ilimin yara mata, yana mai cewa saka hannun jari a fannin zai taimaka wajen ci gaba da rage talauci
  • Jakadan Tarayyar Turai, Gautier Mignot, ya tabbatar da aniyar ƙungiyar na ci gaba da tallafawa shirye-shiryen ilimi, lafiya da tsaro a Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya buƙaci Tarayyar Turai ta faɗaɗa tallafin da take bai wa Kano da Najeriya.

Basaraken ya jero muhimman fannoni da ke bukatar tallafin wadanda suka haɗa da tsaro, kiwon lafiya da ilimi da sauransu.

Sarki Sanusi II ya roki alfarma a wurin EU
Sarki Muhammadu Sanusi II, yayin ganawa da Mataimakin Shugaban Bankin European Investment Bank, Lexembourg a Lagos. Hoto: Sarauta TV.
Source: Facebook

Basaraken ya fi mayar da hankali kan buƙatar ƙarin saka hannun jari a ilimin yara mata, yana mai bayyana hakan a matsayin ginshiƙi na ci gaba mai ɗorewa da bunƙasar al’umma, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Sarki Muhammadu Sanusi II ya umarci rufe wani babban otal a Kano

Tasirin jihar Kano a bangarori da dama

Sarki Sanusi II ya ce Kano ta daɗe tana da muhimmiyar matsayi a harkokin kasuwanci, al’adu da wayewa tun zamanin cinikin Sahara, saboda haka tana buƙatar ƙarin haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa.

Ya ƙara da cewa saka hannun jari a ilimi, musamman ilimin yara mata, na daga cikin hanyoyin da suka fi tasiri wajen bunƙasa ci gaba da rage talauci.

Sarkin ya kuma bayyana cewa akwai buƙatar tallafi domin ƙarfafa tsarin kiwon lafiya da kuma magance matsalolin tsaro da ke addabar al’ummomi a Arewacin Najeriya.

Ya ce haɗin gwiwa mai ƙarfi tsakanin abokan hulɗar ƙasa da ƙasa da cibiyoyin cikin gida zai taimaka wajen hanzarta ci gaba da inganta rayuwar jama’a.

Sarki Sanusi II ya magantu kan manyan matsalolin Kano
Sarki Muhammadu Sanusi II yayin rangadi a Kano. Hoto: Sanusi II Dynasty.
Source: Facebook

Martanin Jakadan EU game da Arewa

A yayin ziyarar Jakadan Tarayyar Turai a Najeriya, Gautier Mignot, da tawagarsa zuwa masarautar Kano, Sarkin ya shirya ƙaramar hawan sallah na girmamawa a fadarsa.

Bikin ya nuna kyawawan al’adun masarautar Kano tare da haskaka muhimmiyar rawar da Kano ta taka a tarihin kasuwanci, al’adu da wayewa a Yammacin Afirka.

Kara karanta wannan

2027: Salon Peter Obi ya fita daban, ya bayyana tsare-tsarensa ga Najeriya

An saka Hawan Kano cikin jerin al’adun duniya na UNESCO a shekarar 2024 saboda muhimmancinsa ga al’adu da kuma darajarsa a duniya.

Da yake mayar da martani, Mignot ya ce ziyarar tasu wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙarfafa haɗin gwiwa da Arewacin Najeriya kan batutuwan ci gaba masu muhimmanci.

Ya sake tabbatar da aniyar Tarayyar Turai na tallafawa shirye-shiryen da ke inganta samun ilimi, kiwon lafiya da tsaro a yankin, cewar Tribune.

Sarki Sanusi II ya ba Arewa shawara

An ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bukaci shugabanni su mayar da hankali kan aiwatar da ayyuka maimakon yawan sanarwar za su yi aikin.

Ya nuna damuwa kan yadda talauci, rashin ingantaccen ilimi da matsalolin kiwon lafiya ke ci gaba da addabar miliyoyin mutane a Arewa maso Yamma.

Sarkin ya bayyana haka ne a wani muhimmin zama da jagororin yankin suka yi a jihar Kano domin nemo mafita a kan matsalolin da suka dame su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.