Sarkin yawa ya fi sarkin karfi: Jama’an jahar Katsina sun kashe wasu barayin mutane 3 har lahira

Sarkin yawa ya fi sarkin karfi: Jama’an jahar Katsina sun kashe wasu barayin mutane 3 har lahira

Jama’a wani kauyen jahar Katsina, Dallawar Mahauta sun fusata sakamakon yawaitan ayyukan yan bindiga masu garkuwa da mutane a yankinsu, a wannan lokaci sun dauki mataki da kansu inda suka yi halaka wasu barayin mutane guda uku.

Majiyar Legit.com ta ruwaito lamarin ya faru ne ranar Talata 11 ga watan Disamba a kauyen dake cikin karamar hukumar Dandume ta jahar Katsina, a lokacin da yan bindigan suka yi kokarin satar wani mashahurin attajiri a kauye, Alhaji Abdulrahman Dallawar mahauta.

KU KARANTA: Masu yi don Allah: Babban jami’in kwastam ya yi fatali da tayin cin hancin naira miliyan 50

Sai dai duk da cewa yan bindigan sun shigo kauyen ne akan babura sama da ashirin goyon bibbiyu, amma duk da yawansu basu samu nasarar sace attajirin ba saboda sun kasa gane inda yake, amma sai suka yi kokarin sace dansa.

Bayan da jama’an kauyen suka lura yan bindigan sun daina harbe harbe, sai suka yi musu kwantan bauna, daga nan suka far ma yan bindigan, inda suka kashe mutum uku daga cikinsu nan take, sai dai an kashe wani dan kauyen, Yushau tare da jikkata mutane biyu daga cikinsu.

Daga bisani jami’an Yansanda da suka garzaya kauyen sun dauke gawarwakin miyagun mutanen da aka kashe zuwa babban ofishin Yansandan Najeriya dake garin Dandume, inda bayan wani dan lokaci suka mikasu ga babban asibitin garin Funtua.

Da majiyarmu ta tuntubi kaakakin rundunar Yansandan jahar Katsina, SP Gambo Isah domin jin ta bakinsa game da wannan artabu tsakanin jama’an kauyen Dallar mahauta da yan bindiga, sai yace ta saurara zasu fitar da jawabi game da hakan.

A wani labarin kuma Sojoji sun kama wasu mutane guda uku dauke da manyan bindigu guda arba’in da hudu yayin da suke kokarin shigar dasu jahar Zamfara daga jahar Neja, ta kauyen Bena dake cikin karamar hukumar Wasagu ta jahar Kebbi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel