Ana Jimamin Janar Rabe, Sarki Ya Sake Mutuwa a hannun 'Yan Bindiga

Ana Jimamin Janar Rabe, Sarki Ya Sake Mutuwa a hannun 'Yan Bindiga

  • Wani basarake da 'yan bindiga suka yi garkuwa da shi a jihar Kwara ya rasu duk da cewa iyalansa sun biya Naira miliyan 18 kuɗin fansa
  • Lamarin ya tayar da hankali kan ƙaruwar sace-sacen sarakunan gargajiya da manyan mutane a yankin da ke fama da matsaloli a kwanakin nan
  • Rahoto ya ce hukumomin tsaro a Kwara sun fara farautar masu garkuwar domin kama su bayan mutuwar basaraken cikin yanayi mai ban tausayi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kwara - Wani basarake a jihar Kwara ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane duk da cewa iyalansa sun biya Naira miliyan 18 domin a sake shi.

An sace basaraken ne da bindiga, inda masu garkuwar suka nemi kuɗin fansa kafin su sake shi, amma bai tsira daga zaman da ya yi a hannunsu ba duk da biyan kuɗin.

Kara karanta wannan

Yadda aka karbo gawar Manjo Janar Rabe Abubakar bayan ya rasu a hannun 'yan Bindiga

Sarkin da ya mutu a hannun 'yan bindiga a Kwara
Sarkin da ya rasu a wajen masu garkuwa a hagu da sojoji a dama. Hoto: HQ Nigerian Army|Illorin Parrot
Source: Facebook

Vanguard ta wallafa cewa mutuwarsa ta girgiza al’ummarsa tare da sake jawo damuwa kan yadda ake ƙara kai hare-hare da sace sarakunan gargajiya a yankin Arewa ta Tsakiya.

An fara neman masu garkuwar

Jami’an tsaro a jihar Kwara sun fara farautar waɗanda ake zargi da yin garkuwa da basaraken bayan wannan mummunan lamari.

Lamarin ya jawo Allah-wadai daga shugabannin al’umma da mazauna yankin, waɗanda suka bayyana kisan a matsayin rashin tausayi, tare da kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar an gurfanar da su.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Gwamnatin jihar Kwara ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan mutuwar basaraken ba.

Kisan ya ƙara shiga jerin sarakunan gargajiya da ƙungiyoyin masu laifi suka kai wa hari tare da neman kuɗin fansa a jihohi daban-daban na Najeriya.

Kudin da aka ba ’yan bindiga

An kuma tattaro cewa al’ummar yankin sun sayi sababbin babura guda biyu tare da samar da lita 100 na fetur kamar yadda masu garkuwar suka buƙata, amma duk da haka ba a sake shi ba.

Kara karanta wannan

Bincike: 'Yan bindiga ne suka mika gawar Janar Rabe hannu da hannu? Gaskiya ta fito

Daily Trust ta rahoto cewa a lokacin da mutanen yankin suka nemi yin magana da basaraken, masu garkuwar sun sake neman ƙarin kuɗi, wanda ya sa aka fara zargin cewa ya mutu tun yana cikin maboyarsu.

Taswirar jihar Kwara
Taswirar jihar Kwara a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Yadda aka sanar da mutuwar sarkin

Majiyoyi sun ce an sanar da mutuwarsa ne ta wani saƙon murya da aka samu daga wani mamba na kwamitin yankin da ke cikin ƙoƙarin ganin an kuɓutar da shi.

A cikin saƙon, mamban kwamitin ya sanar da mazauna yankin cewa duk ƙoƙarin da iyalai, shugabannin al’umma, malamai da sauran masu ruwa da tsaki suka yi bai yi nasarar dawo da basaraken da rai ba.

Ya ce:

“Wannan sanarwa ce ga al’ummar Olayinka baki ɗaya, maza da mata, manya da yara, cewa uban kasa da muke so, Mai Martaba Alhaji Olatunji, Sarkin Olayinka, ya amsa kiran mahaliccinsa. Kaddara ta riga fata.”

Janar Rabe ya mutu a daji

A wani labarin, mun kawo muku cewa Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da cewa Janar Rabe Abubakar (Mai ritaya) da aka yi garkuwa da shi ya rasu.

A sanarwar da Gwamnatin Katsina ta fitar ta nuna cewa ba masu garkuwar ba ne suka kashe shi kai tsaye, inda ta ce wasu cututtuka ne suka yi sanadinsa.

Daga baya an ceto matar shi da aka yi garkuwa da ita a lokacin da suke tafiya tare, sai dai kuma wasu daga cikin iyalan shi sun karyata rashin lafiyar da aka jingina masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng