An yi garkuwa da 'Diyar Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Katsina

An yi garkuwa da 'Diyar Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Katsina

Mun samu cewa a halin yanzu diyar shugaban jam'iyyar PDP na karamar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina, ta shiga hannun 'yan ta'adda masu garkuwa da mutane yayin da suka yi awon gaba da ita a daren jiya na Laraba.

Rahotanni sun bayyana cewa, 'yan ta'adda sun yi awon gaba da Zainab Hussaini a gidansu da ke kauyen Maitsani daura da babbar hanyar garin Dustinma bayan dare ya raba kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito.

Binciken manema labarai ya tabbatar da cewa, 'yan ta'addan rike da bindugu sun afka gidan shugaban jam'iyyar, Hussaini Maitsani, inda suka yi arangama da sabani na rashin sa da ya sanya suka yi awon gaba da diyarsa.

An yi garkuwa da 'Diyar Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Katsina

An yi garkuwa da 'Diyar Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Katsina
Source: UGC

Wata majiyar rahoton ta bayyana cewa, wannan wannan budurwa ba ta kasance haifaffar ga shugaban jam'iyyar ba kasancewarta diya ga dan uwansa da kawo ba bu amo ballanatana labari dangane da bukatar 'yan ta'adda.

KARANTA KUMA: Boko Haram: Buhari zai gana da shugabannin kasashe 5 a Kasar Chadi

Tuni bincike ya kankama yayin da kungiyoyin sa kai na kauyen Maitsani suka bazama wajen neman cimma nasara ta ceto wannnan budurwa domin sada da 'yan uwanta.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, rayuwar wani mai garkuwa da mutane ta salwanta yayin hukumar 'yan sanda ta ciyo wani bayan sun tafka bakin gumurzu na fafatawa ta musayar wuta.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel