Yadda wata matar aure ta shirya sace kanta da kanta a jihar Neja

Yadda wata matar aure ta shirya sace kanta da kanta a jihar Neja

Wata matan aure mai suna Habiba Usman mai shekaru 20 a duniya ta hada baki da wasu samari biyu da niyyar sace kanta da kanta domin karbar kudin fansa daga mijinta mai suna Malam Usman Alfa.

Habiba wacce ke dauke da juna biyu ta bar gidan mijinta da ke garin Beji a karamar hukumar Bosso na jihar Neja ne da niyyar zuwa asibitin Minna domin awon ciki a ranar 28 ga watan Disamba amma ba ta dawo ba.

Daily Trust ta ruwaito cewa anyi kokarin gano inda ta ke amma ba a ganta ba hakan yasa mijin ya sanar da iyayen matar domin suma su taya shi neman ta amma duka ba a dace ba.

Yadda wata matar aure ta shirya sace kanta da kanta a jihar Neja

Yadda wata matar aure ta shirya sace kanta da kanta a jihar Neja
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: 2019: Wani babban basaraken arewa ya yi barazanar tsinewa 'yan siyasa

"A daren ranar da ta bace, an kira mijinta a waya inda aka bukaci ya biya N4 miliyan a matsayin kudin fansa muddin yana son ya sake ganin matarsa," inji majiyar.

Mijin tare da taimakon 'yan uwanta sun roki wanda su kayi garkuwa da ita har suka rage kudin zuwa N150,000 kuma aka biya su kafin suka sako matar.

Sai dai kafin biyan kudin, mijin matar ya riga ya sanar da jami'an 'yan sanda inda suka gano cewa anyi kirar wayar ne daga karamar hukumar Sarkin Pawa na jihar Neja daga bisani kuma masu wayar suka koma garin Tunga duk a jihar Minna.

"An kama mutane biyu da ake zargi da hannu cikin sace matar, Umar Abubakar dan asalin karamar hukumar Chanchaga da Musa Abubakar daga garin Sauka Kahuta a Minna.

"Da bincike ya yi nisa, an gano cewar matar ne ta hada baki da mutanen biyu su sace ta domin su samu kudin fansa daga mijinta," a cewar kakakin 'yan sanda, DSP Mohammed Dan-Inna Abubakar.

Ya tabbatar da cewa matasan sun karbi N150,000 kafin a saki matar sai dai a halin yanzu an samu N140,850 daga hannunsu a matsayin hujja. Ana cigaba da bincike a halin yanzu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel