Alhaji Sanda Kaita ya bar Duniya yana da shekaru 88

Alhaji Sanda Kaita ya bar Duniya yana da shekaru 88

Ba da dadewa bane labari ya zo mana daga wata Jaridar cikin gida cewa, mutanen Jihar Katsina sun yi rashin daya daga cikin manyan Dattawan kasar nan da aka sani watau Alhaji Sanda Kaita.

Alhaji Sanda Kaita ya rasu ne a jiya Ranar Talatar nan watau 25 ga Watan Disamban 2018 yana mai shekara fiye da 80 da haihuwa. Kaita ya cika ne cikin dare, da ke cikin Unguwar Filin Samji da ke Garin Katsina.

Kamar yadda mu ka ji labari, Marigayin ya bar Iyali wanda su ka hada da matan sa 3 da kuma yara fiye da 20. Marigayi Alhaji Kaita ya kuma rasu ya bar jikoki rututu a Duniya. An yi jana’izar sa ne tun a jiya da yamma.

KU KARANTA: An koka bayan an kashe Sojojin Najeriya a Yobe

Daily Trust ta rahoto cewa an bizne Dattijon a gidan na sa da ke bayan wata cibiya mais una Social Development Training Centre a cikin Filin Samji a Jihar Katsina. Sanda Kaita yana cikin manyan da ake da su a Jihar.

Alhaji Sanda Kaita tsohon ‘Dan Boko ne wanda ya taba rike shugabancin fitacciyar makarantar nan ta Katsina watau Government College (GCK) wanda ta reni manyan shugabannin da aka yi a kasar nan da-dama.

Kamar yadda mu ka ji, Marigayin yayi fama da ‘yar rashin lafiya kafin ajali ya riske sa a kan gadon sa. Kaita ya cika yana mai shekaru 88 da haihuwa a Duniya kuma tuni aka bizne sa jiya bayan faduwar rana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel