Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mutane 15 a Neja

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mutane 15 a Neja

Daily Trust ta rahoto cewa wasu ‘yan bindiga dadi sun sace mutane akalla 15 a Ranar Talatar nan da ta gabata a wani Gari da ake kira Garin Mangwaro wanda ya ke kan iyaka da Kaduna a cikin Jihar Neja.

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da mutane 15 a Neja

Garkuwa da mutane yana nema ya zama ruwan dare a Najeriya
Source: Depositphotos

Kamar yadda labari ya zo mana, an sace wadannan Bayin Allah ne a kan hanyar su ta zuwa Garin Kaduna. Kwamishinan yada labarai na Jihar Neja, Danjuma Sallau, ya tabbatarwa ‘yan jarida da aukuwa wannan abu a jiya Laraba.

Danjuma Sallau ya bayyana cewa mutane 10 daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, sun fito ne daga Garin Gwada da ke cikin karamar hukumar Shiroro. Sauran mutanen kuma sun fito ne daga cikin wani kauye a Munya a Jihar Neja.

KU KARANTA: Gwamna Yari yana wata kasa yayin da ake lashe jama’a a Jihar Zamfara

Gwamnatin jihar Neja ta bayyana cewa ta na kokari wajen kubuto da wadannan mutane da aka yi gaba da su. Yanzu haka an yi aika jami’an tsaro na ‘Yan sanda da Sojoji da kuma sauran ‘yan kato da gora zuwa cikin Garin Sarkin Pawa.

Muhammad Abubakar Dan- Inna, wanda shi ne jami’in da ke magana da yawun bakin ‘yan sanda ya tabbatar mana da cewa an aika runduna guda zuwa Garin Munya, yankin da abin ya faru, domin ayi kokarin kubuto da wadannan mutane.

Jiya mu ka ji labari cewa an sake kai wani hari a Jihar Yobe da ke Arewa maso Gabashin Najeriya. ‘Yan ta’addan Boko Haram da su ka fitini yankin sun yi ta’adi ne a wani gari da ke kusa da Damaturu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel