An kama masu garkuwa da mutane da fashi da makami Katsina

An kama masu garkuwa da mutane da fashi da makami Katsina

Rundunar 'yan sanda reshen jihar Katsina ta sanar da samun nasarar kama wasu mutane biyu da suka garkuwa da wata dattijuwa a karamar hukumar Safana.

A wani jawabi da ya yi ga manema labarai a hedkwatar 'yan sanda ta jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce sun kama 'yan ta'addar biyu ne bayan samun bayanan sirri.

Ya ce masu mutanen sun amsa laifinsu, kuma matar da suka yi garkuwa da ita ta tabbatar da cewar sune suka sace ta.

Kazalika, Isah ya ce sun yi nasarar kama wani dan fashi tare da kwace wata mota kirar Toyota Highlander da ya yi fashinta.

An kama masu garkuwa da mutane da fashi da makami Katsina
Kakakin rundunar na kasa; Jimoh Moshood
Asali: Twitter

"A ranar 7 ga watan Janairu jami'an 'yan sanda suka yi nasarar kama wani matashi, Mohammed Sani, mai shekaru 28 dan asalin karamar hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa da wata motar sata yayin da yake kokarin tsallaka wa zuwa janhuriyar Nijar," a cewar Isah.

Kakakin ya ce motar kirar Toyota Highlander mai launin tasa, na dauke da lambar mallaka kamar haka; ABC 572 RN da kuma lambar kira JTEEP21A560186921.

DUBA WANNAN: Tsohon hadimin Tinubu ya zama sabon kwamishinan 'yan sanda a Legas

Isah ya kara da cewa matashin ya amsa laifinsa tare da shaida wa rundunar 'yan sanda cewar ya yi fashin motar ne a garin Jos, jihar Filato.

Rundunar 'yan sanda ta ce tana gudanar da bincike a kan dan fashin, wanda da zarar ta kammala zata gurfanar da shi a gaban kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel