Gwamnatin Tinubu Ta Waiwayi Masu Yada Labaran 'Yan Bindiga a Midiya a Najeriya

Gwamnatin Tinubu Ta Waiwayi Masu Yada Labaran 'Yan Bindiga a Midiya a Najeriya

  • Gwamnatin Tarayya ta bukaci ’yan jarida su daina yawan yada labaran ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a shafukansu
  • Ministan Yada Labarai, Mohammed Idris, ya ce hakan na taimakawa masu aikata miyagun laifuffuka wajen samun farin jini
  • Mohammwd ya bukaci kafafen yada labarai su fi haskaka nasarorin da jami’an tsaro ke samu a yakin da suke da ayyukan ta'addanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Gwamnatin Tarayya ta bukaci kafafen yada labarai da ’yan jarida su fifita zaman lafiya da kishin kasa ta hanyar rage yada ayyukan ’yan ta’adda, ’yan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuffuka.

Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan ranar Alhamis a Abuja a wurin taron tsaro da Kungiyar ’Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) ta shirya tare da hadin gwiwar Hukumar Tsaro ta DSS.

Kara karanta wannan

APC ta yi magana da 'yan majalisa suka fara maganar Tinubu ya sauka

Mohammed Idris.
Ministan yada labarai da wayar da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris Hoto: @HMMohammedIdris
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta rahoto cewa taron mai taken “Kafafen Yada Labarai da Hukumomin Tsaro a Matsayin Abokan Hulda Wajen Gina Kasa” ya tattaro masu ruwa da tsaki daga bangarori daban-daban.

Gwamnatin Tinubu ta ja hankalin yan jarida

Idris ya ce duk da cewa gwamnati na mutunta ’yancin aikin jarida, akwai bukatar a rika amfani da wannan ’yanci cikin hikima domin kauce wa bai wa masu laifi damar yada tsoronsu.

Mohammed Idris ya ce:

“Eh, dole ne mu yi aikinmu kuma mu ruwaito abin da ya faru, amma mafi kyawun dan jarida ko edita shi ne wanda ya san abin da bai kamata ya wallafa ba saboda ci gaban kasa.
“Don Allah ku cire wadannan ’yan ta’adda da masu laifi daga manyan kanun labaranku. Wannan shi ne abin da suke nema kyauta.”

Muhimman tsaro ga aikin jarida

A cewarsa, abin takaici ne yadda wasu kafafen yada labarai ke bai wa ayyukan masu tada kayar baya muhimmanci fiye da nasarorin da jami’an tsaro ke samu.

Kara karanta wannan

An bukaci Shugaba Tinubu ya ayyana wani shirin watanni 6 don magance matsalolin Najeriya

Ministan ya jaddada cewa babu yadda kafafen yada labarai za su yi aiki yadda ya kamata idan babu zaman lafiya da tsaro a kasa, cewar rahoton Premium Times.

Ya yi nuni da nasarorin da aka samu a baya-bayan nan, ciki har da kashe wasu ’yan ta’adda da ’yan bindiga, ceto wadanda aka sace da kuma rusa maboyar miyagu.

Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana jawabi a gidan gwamnatin Najeriya Hoto: @onanuga1956
Source: Twitter

An gargadi gidajen jaridu a Najeriya

Ya gargadi kafafen yada labarai da su guji yada bayanan da ba a tabbatar da sahihancinsu ba ko kuma wallafa rahotannin da za su iya kawo cikas ga ayyukan tsaro.

“Tsaron kasa ba zai amfana ba idan aka yada bayanan da ba a tantance ba. Haka kuma ba zai amfana ba idan aka yi watsi da damuwar jama’a,” in ji shi.

Minsita ya fadi masu taimakon ta'addanci

A wani rahoton, kun ji cewa Ministan Tsaro na Najeriya, Christopher Musa, ya bayyana rukunin mutane biyu da ke kara rura wutar matsalar tsaro kasar nan.

Ya ce masu bada bayanai da ake kira imfoma da masu ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda, ‘yan bindiga da masu tayar da ƙayar baya ne suka sa matsalar tsaro ta ci gaba da ƙamari a ƙasar.

A cewar ministan, ƙungiyoyin ta’addanci da ‘ yan bindiga suna samun damar ci gaba da ayyukansu ne saboda wasu daga cikin jama’a na ba su taimako.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262