Matashiya 'yar shekara 15 ta sayar ta kanenta biyu a kan N800,000, ta fadi dalili
- Hukumar 'yan sanda sum damke wata yarinya mai shekaru 15 da ta sayar da kanenta domin samun kudin biyan jarabawar kammala sakandire
- Yarinyar ta tambayi iyayenta kudin jarabawar ne amma suka fada mata basu da kudi sai dai ta sato yara a sayar kafin a biya mata kudin jarabawar
- Hakan yasa yarinyar ta koma garinsu da sato wasu 'yan uwanta biyu ta mika su ga mahaifinta shi kuma ya sayar da su kan kudi N800,000
Jami'an 'yan sanda reshen jihar Imo sun damke wani matashi dan makarantar sakandire mai shekaru 15, Precious Ehiedo da wasu abokansa biyu, Juliet Ogben da Favour Okoh bisa laifin sayar da kanensa masu shekuru 2 da 7 a kan kudi N800,000.
A yayin da ya ke mika daya daga cikin yaran ga iyayenta a garin Owerri, Kwamishinan 'yan sanda na jihar, Dasuki Galadanci ya ce Precious ta sace Chiemerem Nwoke da Mmesoma Nwoke ne a ranar 13 ga watan Nuwamban 2018 a karamar hukumar Mbano na jihar Imo.
DUBA WANNAN: ISIS na fushi da Boko Haram bayan sun gaza kafa daular musulunci a Najeriya
Kwamishinan ya ce Precious ta tambayi iyayenta kudin jarabawar kammala sakandire (WASSCE) ne amma wai sai iyayenta suka ce ta sace yaran ta sayar domin ta samu kudin jarabawar.
Shugaban 'yan sandan ya ce, "Precious ce ta sato yaran daga karamar hukumar Ehime Mbano na jihar Imo kuma daga bisani ta mika su ga mahaifinta a kasuwar Amaraku."
"An sayar da yaran biyu ga watan Mama Joy a kan kudi N800,000. Mama Joy da wata Favour Okoh sun sayar da yaran ga wata Juliet Ogbor a kan kudi N750,000."
Kwamishan ya ce bayanan sirri da suka samu na ya sanya suka gano daya daga cikin yaran a ranar 15 ga watan Disambar 2018 a garin Agbor na jihar Delta.
Ya ce jami'an 'yan sandan za su cigaba da fadada bincike domin gano dayan yaron.
Galadanci ya ce sayar da dan adam babban zalunci ne musamman yara ma kuma hukumar za ta mika masu laifin ga kotu domin su fuskanci hukunci da zarar an kammala bincike.
Asali: Legit.ng