Wani Limamin Masallaci ya yi garkuwa da bawan Allah, har sai da ya kasheshi

Wani Limamin Masallaci ya yi garkuwa da bawan Allah, har sai da ya kasheshi

Rundunar Yansandan jahar Osun ta yi ram da wani Limamin Masallaci da abokansa guda uku da laifin satar wani mutum, Victor Akinbile tare da kasheshi ba tare da wani hakki ba, sai dai kawai don ya kasa biyansu naira miliyan uku kudin fansa.

Majiyar Legit.com ta ruwaito kwamishinan Yansandan jahar, Fimihan Adeoye ne ya sanar da haka ne a ranar Talata 4 ga watan Nuwamba inda ya bayyana sunayen mutanen kamar Liman Bashir Owolabi, Rafiu Ahmed, Sunday Kayode da Rasheed Waheed.

KU KARANTA: Ashsha! Motar daukan kaya ta kufce ma direba, ta tattake mutum 10 har lahira

A cewar kwamishina Fimihan mutanen sun aikata laifinne a ranar 27 ga watan Nuwamba a gidansa dake cikin karamar hukumar Ifelodun, inda yace sun yi garkuwa da Akinbile ne a ranar Talata 27 ga watan Nuwamba ranar daya baro Legas zuwa Osun don kai ma kakarsa ziyara.

Bayan sun yi garkuwa da Akinbile ne, sai suka tilasta masa ya basu naira miliyan biyar a matsayin kudin fansa, inda nan take ya tura musu naira miliyan biyar cikin asusun guda daga cikinsu, daga bisani kuma suka kaishi bayan gari, suka sanyashi a cikin sundukin motar, suka banka mata wuta.

Kwamishinan ya bayyana cewa Liman Bashir Owolabi, wanda ke gadin gidan dake makwabtaka da gidan kakar Akinbile ne ya bayyana ma sauran mutane ukun cewa Akinbile ya shigo gari, zuwa yanzu dai dukkanin mutanen sun amsa laifinsu, banda Bashir, wanda yace sharri ake masa.

“Wasu abokan Akinbile ne suka kawo mana rahoto bayan sun kai har karfe 10:30 na dare suna neman sa basu ganshi ba, bayan nan ne suka gano ya tura ma wani bakon suna kudi naira miliyan uku a asusun bankin UBA.

“Da samun labarin sai muka shiga farautan miyagun mutanen, a haka muka kama Rafiu Ahmed a Legas a unguwar Ikorodu, Rafiu ne ya yi mana jagora zuwa kama sauran mutanen uku, a gaskiya ba zamu sassauta musu ba saboda sun yi ma mamacin kisan wulakanci.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel