Saudiyya Ta Shigo da Tulin Kayan Abinci Najeriya domin Raba wa Talakawa
- Gidauniyar da ke raba tallafi a kasar Saudiyya tare da hadin gwiwar NEMA da gwamnatin Yobe sun raba kayan tallafi ga iyalai 6,000 a jihar
- Bayan jihar Yobe, an bayyana cewa gidauniyar ta bayar da karin kaya da dama domin rabawa masu buƙata a wasu jihohi biyar a kasar nan
- A lokacin kaddamar da rabon, gwamnatin Yobe ta ce za ta tabbatar da an raba kayan cikin gaskiya da adalci kuma ga waɗanda suka dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Yobe - Cibiyar ba da agaji da jin ƙai ta Sarki Salman ta ƙasar Saudiyya ta kaddamar da raba kayan abinci a tarayyar Najeriya.
An yi rabon ne tare da haɗin gwiwar hukumar NEMA da gwamnatin Yobe, inda aka raba kayan abinci da kayayyakin agaji ga gidaje 6,000 da ambaliya da sauran bala'o'i suka shafa a faɗin jihar.

Source: Facebook
Legit Hausa ta gano cewa hukumar NEMA ta wallafa hotunan kayan abinci da aka raba a jihar Yobe a wani sako da ta wallafa a shafinta na X.
Yadda aka raba abincin Saudi
Shugabar NEMA, Zubaida Umar, ta bayyana cewa an ƙaddamar da rabon kayan agajin ne ga mabukata a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Zubaida Umar ta ce shirin na da nufin tallafa wa al'ummomin da ke da rauni tare da ƙarfafa ayyukan bayar da agajin gaggawa a yankunan da bala'o'i suka shafa.
Ta bayyana cewa ƙungiyar agajin ta Saudiyya ta bayar da kwandunan abinci guda 24,302 ga Najeriya domin rabawa mabukata a jihohin Yobe, Benue, Anambra, Kebbi da Taraba.
A cewarta, gidaje 6,000 da aka tantance a jihar Yobe ne za su amfana a wannan mataki na shirin kafin daga bisani a wuce wasu jihohii.
Karin bayani kan tallafin
Shugabar NEMA ta ƙara da cewa irin waɗannan shirye-shiryen da cibiyar ta aiwatar a baya sun samar da muhimman kayan agaji ga mutanen da suka rasa matsugunansu da sauransu.
Yayin da take kira ga hukumomin da ke aiwatar da shirin da su bi ƙa'idojin aiki da aka gindaya, Zubaida Umar ta jaddada muhimmancin gaskiya da riƙon amana a dukkan matakan rabon kayan.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa ta ce:
"Ya kamata a gudanar da rabon kayan ne bisa ƙa'idojin da KSrelief da NEMA suka shimfiɗa domin tabbatar da gaskiya, adalci da kuma isar da kayan ga waɗanda aka nufa yadda ya kamata,"
Da yake mayar da martani, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, wanda Dr Mohammed Goje, ya wakilta, ya bayyana tallafin a matsayin wanda ya zo a kan lokaci kuma abin yabawa.
Za a raba abinci a Ekiti
A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar Yiaga Africa ta yi bayyana cewa wasu 'yan siyasa sun tanadi abinci domin rabawa talakawa a Ekiti.
Kungiyar ta ce an tanadi shinkafa, taliyar Indomi, kudi da sauransu domin a ba talakawa su yi zabe a zaben gwamnan da za a yi a Ekiti a ranar Asabar.
Yiaga ta gargadi talakawa da su guji sayar da kuri'unsu domin hakan zai iya zama ci baya ga harkokin dimokuradiyya da gudanar da mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

